Home Back

Hukumar Kwastam Za Ta Dauki Matakin da Zai Kawo Saukin Kayan Abinci a Najeriya

legit.ng 2024/7/6
  • Hukumar kwastam ta kasa ta yi alwashin kawo karshen matsalar boye abinci da ta addabi daukacin al'ummar Najeriya
  • Kwastam ta ce a yanzu haka ta dauki masu matakai wanda za su kawo karshen matsalar domin kawo saukin rayuwa
  • Shugaban hukumar ta kasa, Wale Adeniyi ne ya bayyana haka yayin da yake bayyana nasarorin da ya samu a shekara daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukumar kwastam ta bayyana matakin da ta dauka domin kawo karshen boye abinci a Najeriya.

Hukumar ta tabbatar da cewa boye abinci na cikin matsalolin da suke kawo tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.

Hukumar kwastam
Hukumar kwastam za ta cigaba da daukan mataki kan masu boye abinci. Hoto: Nigeria Customs Service Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban hukumar ya fadi haka ne yayin da yake magana bayan cika shekara daya da naɗa shi da Bola Tinubu ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsadar abinci: Matakin da kwastam ta dauka

Shugaban hukumar kwastam, Wale Adeniyi ya ce sun kammala dukkan shirye shiryen ganin masu boye abinci ba su samu nasara ba a Najeriya.

Wale Adeniyi ya ce kwace shinkafa da hatsi da ya kai kimanin Naira biliyan 4.4 a wajen wadanda suka boye abinci yana cikin matakan da suka dauka.

Ya kuma tabbatar da cewa kokarin yin hakan na cikin ayyukan da suke yi domin samar da sauki a kasa da kawo zaman lafiya.

Kwastam za ta saukaka shigo da magani

Har ila yau shugaban hukumar ya ce za su cigaba da haɗaka da ma'aikatar lafiya ta kasa domin samun shigo da kayan magani cikin sauki.

Wale Adeniyi ya ce yin hakan na nufin samar da kayan cikin sauki domin al'umma su rika saye a farashi mai rahusa, rahoton NAN.

Ya kuma tabbatar da cewa hakan na cikin kokarin da shugaba Bola Tinubu ya ke wajen ganin al'ummar Najeriya sun samu sauƙin rayuwa.

Jami'an kwastam sun gano dabarar 'yan kwaya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta koka kan yadda dilolin kwaya ke hada kai da jami'anta wajen samun hanyar safarar kayan maye cikin sauki.

Shugaban hukumar ta kasa, Adewale Adeniyi ne bayyana haka yayin da yake baje-kolin kayan shaye-shaye da suka yi nasarar kamawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading