Man Fetur: An Sake Samun Rikici tsakanin Dangote da NNPCL
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - An samu bayanai mabanbanta kan adadin man fetur da matatar Dangote ta ba kamfanin NNPCL.
Matatar Dangote ta ce ta cigaba da loda tataccen man fetur ga kamfanin NNPCL bayan an fara lodin a ranar Lahadi.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami'in yada labarai a matatar Dangote, Anthony Chiejina ya bayyana adadin da suka ba kamfanin NNPCL.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan fara dibar man fetur a matatar Dangote, kamfanin NNPCL ya ce ya loda mai lita miliyan 16.8.
NNPCL ya ce an samu karanci a kan adadin farko na lita miliyan 25 da matatar Dangote za ta samar.
Matatar Dangote ta fitar da rahoto a kan man fetur da ta fitar ga NNPCL inda ta ce a yanzu ta ba kamfanin mai lita miliyan 111.
Haka zalika, jami'in matatar Dangote, Anthony Chiejina ya ce sun cigaba da loda mai ga kamfanin NNPCL tun ranar Lahadi.
Biyo bayan sabon bayanin da matatar Dangote ta fitar manema labarai sun nemi jin ta bakin NNPCL.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton kamfanin NNPCL bai amsa sakon da aka tura masa ba.
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da yan Najeriya ke cigaba da tsammanin sauki a kan farashin fetur an samu sabani tsakanin NNPCL da matatar Dangote.
An samu bayanai mabanbanta kan yadda cinikin man fetur ya kullu tsakaninsu inda suka fitar da sanarwa mai karo da juna kan yadda suka kulla ciniki.
Asali: Legit.ng