Home Back

YUNƘURIN MAIDA TSOHON SARKI: Gwamnan Kano ya bada umarnin a kama Aminu Ado bayan ya shigo Kano cikin dare

premiumtimesng.com 2024/6/28
YUNƘURIN MAIDA TSOHON SARKI: Gwamnan Kano ya bada umarnin a kama Aminu Ado bayan ya shigo Kano cikin dare

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir-Yusuf ya umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano ya kama tsigaggen sarki Aminu Ado a cikin gaggawa.

Ya bada umarnin a kama shi saboda ya shigo Kano kwana biyu bayan cire shi, domin ya tayar da fitina.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna, Sanusi Bature ya fitar ƙarfe 7 na safiyar Asabar, ya ce an shigo da Aminu cikin Kano da dare a ranar Juma’a, ranar da aka bai wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar shaidar kama mulki.

Hakan na faruwa ne yayin da shi kuma Sarki Sanusi II ya shiga Fadar Sarki ƙarfe 1 na dare, tare da rakiyar Gwamna, Mataimakin sa, Kakakin Majalisa da manyan ƙusoshin gwamnatin Kano, a ranar Asabar, 25 ga Mayu 2024 kenan.

A matsayin Gwamna Abba na Shugaban Tsaron Jihar Kano, ya bada umarni ga Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano ya kama Aminu Ado, saboda tayar da hankula da ƙoƙarin hargitsa zaman lafiya a Kano.

Dama dai tun cikin daren jiya Daily Nigerian ta ruwaito cewa: “Jirgin da aka yi shata ya ɗauki tsigaggen sarki Aminu Ado daga Abuja zuwa Kano.

Rahotonni na cewa ana ƙoƙarin yin amfani da jami’an tsaro domin a maida shi kan mulki da ƙarfin tsiya.”

People are also reading