Home Back

2027: Jam’iyyun Adawa Na Shirin Hadaka a Doke APC, Peter Obi Ya Bayyana Sharudda

legit.ng 2024/7/3
  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya yi karin haske kan maganar hadakarsa da Atiku Abubakar
  • Peter Obi ya ce matuƙar aka samu daidaito kan yadda za a magance matsalolin Najeriya a tsakaninsu zai goyi bayan haɗakar
  • Jawabin Peter Obi ya zo ne bayan wasu maganganu da Atiku Abubakar ya yi kan haɗaka domin kada jam'iyyar APC a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labor a zaben da ya wuce, Peter Obi ya bayyana dalilan da za su sa shi yin haɗaka da PDP a 2027.

Peter Obi and Atiku
Peter Obi ya ce akwai yiwuwar ya yi hadaka da Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Peter Obi ya bayyana haka ne a yayin hira da ya yi da yan jarida.

Jawabin na Peter Obi na zuwa ne bayan wata ziyara da ya kai wa Atiku Abubakar da wasu manyan yan jam'iyyar PDP a kwanakin baya da kuma kiran da Atiku ya yi kan haɗaka tsakaninsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar zai goyi bayan Peter Obi

A kwanakin baya ne tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce idan har aka mika tiketin takarar PDP zuwa kudu maso gabashin Najeriya to zai goyi bayan Peter Obi.

Peter Obi ya yi godiya ga Atiku Abubakar bisa wannan bayani da ya yi kuma ya ce hakan ya kara masa karfin gwuiwa kan yin haɗaka tsakaninsu.

Sharuddan hadakar Peter Obi da Atiku Abubakar

Sai dai a cikin hirar da Peter Obi ya yi, ya bayyana cewa dole ne hadakar ta kasance kan ceto Najeriya a halin da take ciki.

Amma ya ce idan dai kawai za a yi haɗakar ce domin samun damar tsayawa takara a zaɓen 2027 to shi bazai goyi bayanta ba

Peter Obi ba mayen mulki ba ne

Har ila yau Peter Obi ya bayyana cewa shi ba wanda ya damu da dole sai ya mulki Najeriya kota halin ƙaƙa ba ne, rahoton the Cable.

Ya ce shi yana siyasa ne domin ganin ya share wa yan Najeriya hawaye da kawo ayyukan cigaban ƙasa musamman wadanda suka shafi talakawa.

Utomi ya nemi hadakar LP da PDP

A wani rahoton, kun ji cewa jigon siyasa a Najeriya ya bayyana yiwuwar kirkirar sabuwar jam’iyya a Najeriya da ‘yan siyasa za su yi kafin zabe.

Pat Utomi ya ce, akwai bukatar a hada kai tsakanin ‘yan siyasa domin samun shugabanni na gari bayan mulkin APC domin ciyar da kasa gaba.

Asali: Legit.ng

People are also reading