Home Back

Gwamnan Bauchi Ya Sauke Shugaban Riƙo Na Ƙaramar Hukumar Alkaleri Da Mataimakinsa

leadership.ng 2024/6/29
Gwamnan Bauchi Ya Sauke Shugaban Riƙo Na Ƙaramar Hukumar Alkaleri Da Mataimakinsa

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya sallami shugaban ƙaramar hukumar Alƙaleri Hon. Kwamared Bala Ibrahim da mataimakinsa daga muƙamansu.

Korar ta fara aiki ne nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba a cewar fadar gwamnatin jihar.

A wata wasiƙa da ta fito a ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Bauchi Barista Ibrahim Muhammad Kashim, ta nuna cewa “An sallami shugaban riƙon kwarya na ƙaramar hukumar Alƙaleri tare da mataimakinsa baki ɗaya.”

Tuni aka aike da wasiƙar sallamar zuwa ga babbar sakatariyar ma’aikatar ƙananan hukumomi da masarautar gargaji ta jihar Bauchi domin sanar da ma’aikatar wannan matakin.

Sai dai wasiƙar ba ta yi cikakken ƙarin haske kan dalilin ɗaukan wannan matakin ba.

People are also reading