Home Back

Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Da Kwamitocin Bincike Kan Karkatar Da Kadarorin Gwamnati Da Rikicin Siyasa A Jihar

leadership.ng 2024/5/19
Gwamna Yusuf

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wasu kwamitocin bincike guda biyu da za su bankado almubazzaranci, karkatar da dukiyar al’umma, tayar da rikicin siyasa da kuma bacewar wasu mutane a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

A yayin kaddamar da mambobin kwamitocin a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf ya sha alwashin gurfanar da duk wanda aka samu yana da hannu kan wannan badakalar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya tunatar da cewa, wannan yunkurin na daga cikin alkawarin da ya dauka na kaddamar da bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a rikicin siyasa da aka samu a jihar.

Ya ce, “Rikicin siyasa babban koma baya ne ga ci gaban dimokuradiyya a duniya. Yana haifar da asarar rayuka da dukiyoyi tare da rashin aminta da juna daga bangaren al’umma da masu rike da madafun iko.

“Bai kamata a yi watsi da zargin kisan kai da aka yi kan siyasa ba musamman a shekarar 2023, ya zama dole a yi bincike domin hana afkuwar irin lamarin nan gaba.”

Kwamitin farko da ke karkashin Mai Shari’a, Zuwaira Yusuf, zai maida hankali kan binciken shari’o’in tashe-tashen hankula na siyasa da bacewar mutane daga 2015 zuwa 2023.

Kwamitin bincike na biyu da ke karkashin Mai shari’a, Faruk Lawan, zai zurfafa bincike kan almubazzaranci da karkatar da dukiyar al’ummar jihar.

People are also reading