Home Back

Bayern ta tuntubi Rangnick domin maye gurbin Tuchel

bbc.com 2024/5/4
Ralf Rangnick

Asalin hoton, Getty Images

Ralf Rangnick ya ce Bayern Munich ta tuntube shi cewar kungiyar dake buga Bundesliga na son bashi aikin maye gurbin Thomas Tuchel.

Mai horar da Bayern, Thomas Tuchel zai bar Allianz Arena a karshen kakar bana, kuma ana alakanta Rangnick da cewar shi ne zai maye gurbin takwaransa na Jamus.

Rangnick, mai shekara 65 yana horar da tawagar kwallon kafa ta Austria, wadda take shirin shiga gasar Turai ta Euro 2024 da za a yi a Jamus cikin watan Yuni.

Rangnick, wanda ya ja ragamar Manchester United wata shida a matakin rikon kwarya, ya ce duk wani hukuncin da ya yanke ba zai shafi batun kudi ba.

Ana mutanta Rangnick kan aikin da ya gudanar a Jamus, wanda ya horar da Ulm da Stuttgart da Hannover da Hoffenheim da Schalke da kuma RB Leipzig.

Ya lashe German Cup da kai wa daf da karshe a Champions League tare da Schalke a 2011.

Duk wanda ya karbi jan ragamar Bayern Munich, yana jan aiki a gabansa wajen kai ta kan ganiya, wadda ta rasa Bundesliga na bana, bayan daukar 11 a jere.

An yi ta alakanta kociyan Bayern Leverkusen, Xabi Alonso da cewar zai koma aiki da Bayern, wanda daga baya ya fayyace cewar zai ci gaba da horar da Leverkusen.

People are also reading