Home Back

Taimakon Afrika? A Dauki Hakikanin Mataki

leadership.ng 2024/7/6
Taimakon Afrika? A Dauki Hakikanin Mataki

Kusan babu wata kasar da take hulda da kasashen Afirka da ba ta bayyana niyyar taimaka musu wajen samun ci gaban tattalin arziki ba. Sai dai kyan alkawari cikawa. Ya kamata a dauki hakikanin mataki wajen taimakon kasashen Afirka maimakon maganar baka kawai.

Hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, ta fuskar aikin gona, wani misali ne mai kyau kan yadda ake daukar hakikanan matakai wajen raya nahiyar Afirka. A wajen taron kara wa juna sani kan hadin gwiwar Afirka da Sin a fannin fasahohin aikin gona, wanda ya gudana a birnin Sanya na kasar Sin a kwanan baya, masana mahalarta taron na kasashen Afirka da na kasar Sin sun ambaci dimbin sakamakon da aka samu a kokarin yin amfani da fasahohin kasar Sin wajen samar da karin amfanin gona a kasashen Afirka. Misali, irin shinkafar musamman da cibiyar nazarin kimiyya da fasaha masu alaka da aikin gona ta kasar Sin ta ba wasu kasashe 9 dake nahiyar Afirka. Bayan an yi gwajin nomanta, an ga yawan shinkafar da aka samu ya karu da fiye da kashi 20%. A nata bangare, cibiyar nazarin fasahohin aikin gona a wurare masu zafin yanayi ta kasar Sin ta yi kokarin yayata wani sabon nau’in rogo a kasashen Afirka, wanda ya sa yawan rogon da a kan girba ya ninka har sau 4. Haka zalika, a cikin shekaru 10 da suka wuce, an yi amfani da cibiyoyin nuna fasahohin aikin gona na zamani guda 24 da kasar Sin ta kafa a kasashen Afirka, wajen yada wasu fitattun fasahohi fiye da 300, ta yadda yawan amfanin gonar da ake samu bisa matsakaicin matsayi ya karu da kashi 30% zuwa 60%, da haifar da alfanu ga magidanta fiye da miliyan 1 na kasashe daban daban dake nahiyar Afirka…

Ban da samar da karin amfanin gona, fasahohin kasar Sin sun ba da damar bude sabuwar sana’a a kasashen Afirka. Misali, bangaren noman laimar kwado. Da ma a kasar Rwanda, mutane ba su cin laimar kwado. Daga baya an shigar da fasahar noman laimar kwado ta kasar Sin cikin kasar, sa’an nan sannu a hankali, amfanin gonan ya fara samun karbuwa a cikin al’ummar kasar. A halin yanzu, magidanta fiye da 4000 na kasar Rwanda na gudanar da aikin noman laimar kwado, sana’ar da ta samar da guraben aikin yi ga mutane fiye da dubu 30. To, ga shi, laimar kwado ta zama abinci mai gina jiki ga jama’ar kasashen Afirka, har ma ta zame musu wata hanyar samun wadata.

Sai dai bayan da aka samu karin amfanin gona, ya kamata a samu hanyar sayar da su. A wannan fanni, gwamnatin kasar Sin ta sanar da bude hanya mai sauki ga shigowar amfanin gonan kasashen Afirka cikin kasuwannin Sin, a watan Nuwamban shekarar 2021, inda aka rage lokacin da ake bukata wajen tantance ingancin kaya, da yafe wa karin kayayyakin kasashen Afirka harajin kwastam, ta yadda aka ba kasashen Afirka damar sayar da dimbin amfanin gonarsu na musamman a kasar Sin. Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta zama kasa ta biyu a duniya, da aka sayar mata da mafi yawan kayayyakin gonan kasashen Afirka.

Ban da wannan kuma, wani abun da ya fi muhimmanci shi ne, don tabbatar da ci gaba mai dorewa na bangaren aikin gonan kasashen Afirka, ana bukatar samun dimbin matasa ‘yan kasashen Afirka masu kwarewar aiki. A wannan fanni, bisa alkaluman da aka sanar a wajen taron karawa juna sani na wannan karo, cibiyar nazarin kimiyya da fasaha masu alaka da aikin gona ta kasar Sin ta horar da kwararru masu fasahar aikin gona 276 na kasashen Afirka. Kana a nata bangare, jami’ar aikin gona ta Nanjing na kasar Sin ta taimaki kasashen Afirka wajen horar da kwararru masu fasahar noma na matakai daban daban 345, tun daga shekarar 2003…

Ta haka za mu iya ganin cewa, kasar Sin ta dade tana zuba dimbin kudi a kasashen Afirka, da daukar hakikanan matakai a kokarin raya bangaren aikin gona a kasashen, musamman ma a fannonin kyautata fasahohi, da raya sana’o’i, da ingiza bangaren sayayya, gami da horar da kwararru.

Sai dai watakila za ku so ku yi tambaya kan dalilin da ya sa taimakon kasar Sin ga kasashen Afirka cike yake da gaskiya da sahihanci?

Dalili shi ne, domin Sinawa su ma sun taba fama da talauci da yunwa. Kamar yadda tsohon shugaban cibiyar nazarin kimiyya ta nahiyar Afirka, Felix Dakora, wanda shi ma ya halarci taron karawa juna sani na wannan karo, ya fada, kasar Sin ita ma ta taba fuskantar karancin abinci, amma daga bisani ta tabbatar da tsaron abinci, ta hanyar kirkiro sabbin fasahohi a kai a kai, ta yadda take amfani da gonakin da yawansu ya kai kashi 9% na jimillar duniya, wajen samar da abincin da yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 4 na daukacin abincin duniya. Yadda kasar Sin ta samu nasarar raya kanta a lokacin da take fama da koma bayan tattalin arziki, ya sa kasar samun cikakken imani kan cewa, za a iya tabbatar da ci gaban tattalin arziki, ta hanyar hada fasahohin zamani, da ingantattun manufofi, da niyyar aiwatar da manufofi a waje guda, kana mabambantan kasasahe za su iya more ci gaban tattalin arziki tare, gami da samun alfanu na bai daya, yayin da daukacin al’ummar dan Adam ke da damar tabbatar da makomarsu, ta samun ci gaba da wadata na bai daya.

Wani shehun malami na jami’ar Cambridge ta kasar Birtaniya, Ha-Joon Chang, ya bayyana a cikin littafinsa mai taken “tarkon kasashe masu sukuni” da cewa, wasu kasashe masu sukuni sun kwaci dimbin dukiyoyi daga wuraren da suka yi musu mulkin mallaka, don tabbatar da fifikonsu a fannin ci gaban tattalin arziki, daga baya sun yi amfani da dabaru daban daban don neman “cire tsanin da kasashe masu tasowa za su iya amfani da shi wajen hawa sama (Ana nufin samun cikakken ci gaba)”, ta yadda fifikonsu zai dore. To, idan mun iya ci gaba da yin shagube kamar haka, abun da kasar Sin take yi yanzu, shi ne kokarin hadin kai tare da sauran kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka, wajen jingina wani sabon tsani mai inganci a jikin bango, sa’an nan su taka tsanin su hau sama tare, don neman cika burinsu na samun ci gaba na bai daya. (Bello Wang)

People are also reading