Home Back

Sweden ta zargi Iran da kitsa tarzoma a kasarta

dw.com 2024/7/2
Hoto: edna/IMAGO

Sweden ta zargi Iran da amfani da gungun 'yan dabar kasar don tayar da hankalin jama'a, ta hanyar shirya tarzomar kin jinin Isra'ila da Amurka a cikin kasar ta Sweden.

Hukumar leken asirin kasar da kuma rundunar 'yan sandan kasar sun bankado wuraren da suka ce 'yan daban na shirin durfafa, da ma mutanen da suke shirin farwa.

Yanzu haka dai 'yan sanda da sojojin Sweden sun fara wani aikin hadin gwiwa da kasashe daban-daban na duniya, domin dakile wannan shiri, in ji shugaban hukumar leken asirin kasar Daniel Stenling.

People are also reading