Home Back

An yi wa masu bayar da agaji kwantan-bauna a Kwango

dw.com 2024/10/6
Hoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

An kai wani mummunan hari kan ayarin motocin kungiyoyi masu bayar da agaji a lardin Kivu, wani yanki na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ya zama tamkar tungar yaki a tsakanin 'yan tawayen M23 da dakarun gwamnati.

Kungiyar bayar da agaji ta Burtaniya mai suna Tearfund ta sanar a ranar Litinin cewa ta nemi jami'anta na agaji ta rasa bayan wannan hari yayin da jita-jita ke yawo cewa akwai mutum biyu da suka mutum a sakamakon kwantan baunar da aka yi wa masu bayar da agajin.

Kungiyar ta yi kira ga 'yan tawayen M23 da dakarun gwamnati da suka kai zuciya nesa, su samar da sulhu na dindin da zai kawo karshen zubar da jini a arewacin Lardin Kivu wanda ke shaida fitintinu kala-kala tun bayan shekara ta 2021, lokacin da kungiyar M23 ta dawo da kai hare-hare a yankin.

People are also reading