Home Back

Sarautar Kano: Lauyoyi a Arewa Sun Yabawa Hukuncin Kotu, Sun Ba Abba Shawara

legit.ng 2024/8/23
  • Kungiyar Lauyoyi a Arewacin Najeriya ta shawarci Abba Kabir ya yi biyayya ga hukuncin kotu kan masarautu
  • Kungiyar ta ce wannan hukunci ya tabbatar da bin gaskiya da doka bayan rushe masarautun jihar da Abba ya yi
  • Ta kuma bukaci gwamnan ya ba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero hakuri kan wulakanta shi da ya yi a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar Lauyoyi da ke Arewacin Najeriya (NCNLPIA) ta yi martani kan hukuncin kotu game da masarautun jihar.

Kungiyar ta yabawa hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta mayar da Aminu Ado kan kujerar sarauta.

Shugaban kungiyar, Napoleon Otache shi ya bayyana haka a yau Juma'a 21 ga watan Yunin 2024.

Otache ya ce hukunci ya tabbatar da bin doka da oda da kuma kare martabar masarautun.

Ya ce wannan hukunci ya tabbatar da muradun mutanen jihar Kano gaba daya da kuma nuna rashin bin ka'ida na gwamnatin jihar ta yi wurin rusa masarautun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kungiyar ya bukaci Abba Kabir ya ba Aminu Ado Bayero hakuri kan irin cin mutunci da kuma wulakanci da ya yi masa.

Kungiyar ta kuma shawarci Abba Kabir ya tabbatar da yin biyayya ga hukuncin domin samun zaman lafiya a jihar.

Dubban masoya sun tarbi Aminu Ado Bayero

A wani labarin, kun ji cewa a yau Juma'a 21 ga watan Yunin 2024 dubban Kanawa sun tarbi Aminu Ado Bayero.

Dandazon jama'ar sun kuma kai gaisuwar Juma'a ga fadar Sarkin a Nassarawa domin nuna masa goyon baya.

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan rigimar masarautun jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading