Home Back

Gwamnan Zamfara Ya Nemi Karin Tallafi Ga Manyan Makarantun Jihar

leadership.ng 2024/7/3
Gwamnan Zamfara Ya Nemi Karin Tallafi Ga Manyan Makarantun Jihar

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bukaci karin tallafi daga Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na TETFund, domin kammala wasu gine-ginen a manyan makarantun Jihar.

Gwamnan ya yi wannan roko ne a wata ziyarar aiki da ya kai hedikwatar Hukumar ta TETFUND a Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamnan ya bukaci tallafi, musamman ga Jami’ar Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau.

Ya kara da cewa, Jami’ar jihar da ke Karamar Hukumar Talatan Mafara tana da ayyuka da dama wadanda gwamnatocin baya suka fara kuma suka yi watsi da su.

“Lokacin da na ziyarci TETFund, na ambaci cewa a kullum neman kari muke yi. A yau, na zo ne don neman karin tallafi ga wasu manyan makarantun Zamfara.

“Na ziyarci Karamar Hukumar Talata Mafara makonni biyu da suka wuce na ga ayyukan da TETFUnd ta gudanar a Jami’ar Jihar Zamfara. Abin takaici, akwai ayyuka da yawa da aka yi watsi da su a zamanin gwamnatocin baya.

“Muna fuskantar matsaloli game da gyaran Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau, kuma ina bukatar goyon bayanku don warware wannan matsala.

“Zamfara na fama da kalubale daban-daban baya ga matsalar rashin tsaro. Lokacin da muka karɓi mulki a shekarar da ta gabata, ba a biya ma’aikata albashi ba na tsawon watanni uku, kuma dalibanmu ba su iya biyan kudin jarrabawar WAEC da NECO. Har ila yau, muna da dalibai da yawa a kan tallafin karatu a kasashen Cyprus, Indiya, da Sudan wadanda ba a kula da su ba, da sauran batutuwan gaggawa.

“Gwamnatina ta warware matsalar albashin ma’aikata, ta biya bashin da ake bi na WAEC da NECO, sannan ta sasanta tare da daidaita biyan daliban da za su samu tallafin karatu a kasashen waje. Mun zo nan ne domin neman taimakon ku, wanda zai taimaka sosai a kokarinmu na ceto da sake gina Zamfara.”

Da yake mayar da jawabi, Sakataren Zartarwa na Asusun, Arc Sonny T. Echono ya yaba wa Gwamna Lawal bisa nasarorin da ya samu a shekarar farko da ya yi kan mulki.

“Ina so in taya ka murnar cika shekara guda a kan karagar mulki, kuma ina so in yaba maka kan ayyukan da ka ke yi a ma’aikatun gwamnati, cibiyoyi, asibitoci, da sauran fannoni.

“Za mu sake duba bukatar gwamna, kuma mu yi duk mai yiwuwa. Yunkurin da ka ke yi wajen magance al’amuran jihar abin yaba wa ne kuma ya nuna babban matsayi, ni kaina ina so in gode maka kan daidaita bashin WAEC da NECO,” in ji Echono.

People are also reading