Home Back

'Yan Ta'adda Sun Tafka Mummunar Ɓarna, Sun Sace Mutane da Yawa a Babban Titin Kano

legit.ng 2024/7/6

Rahotannin da muka samu ba da jimawa ba sun nuna cewa wasu ƴan ta'adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari babban titin Maiduguri zuwa Kano.

Bayanai sun nuna cewa ƴan ta'addan suna kwashi fasinjoji da dama sun yi awon gaba da su zuwa wurin da ba'a sani ba.

Wasu majiyoyi sun shaidawa Daily Trust cewa maharan sun kai farmakin ne a tsakanin garin Kuturu da Mannanari da ke kan babban titin Maiduguri.

Lamarin ya afku ne da misalin ƙarfe 5:50 na yamma ranar Litinin, inda ƴan ta'addan suka toshe titin kafin daga bisani suka tafi da wasu fasinjoji.

Harin dai ya sa daruruwan matafiya da masu ababen hawa suka tsaya cirko-cirko a sassa biyu na titin wanda mutane ke yawan bi.

Bisa dole matafiyan suka koma kauyukan Benishek da Auno domin su tsira daga sharrin ƴan ta'addan.

"An kai hari tsakanin kauyukan Mannanari da Garin Kuturu, inda wasu mayaƙan Boko Haram suka tsohe ɓangaren motoci masu zuwa, suka sace fasinjoji da dama."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bamu da tabbacin yawan mutanen da maharan suka yi garkuwa da su amma babu shakka an sace mutane da yammacin ranar Litinin," in ji wata majiya.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading