Home Back

Euro 2024: Jamus ta kai zagaye na biyu

bbc.com 2024/7/5
Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images

Mai masaukin baki, Jamus ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta tashi 1-1 da Switzerland a wasa na uku-uku a rukunin farko.

Tun farko Switzerland ce ta fara zura kwallo ta hannun Dan Ndoye, hakan ya sa tawagar ta sa ran ita ce za ta ja ragamar rukunin farko zuwa zagaye na biyu.

To sai dai kuma Jamus ta farke kwallon daf da za a tashi ta hannun Niclas Fullkrug, wanda ya shiga karawar da canjin dan wasa.

Magoya bayan Jamus sun barke da murna da sowa da kuma tafi, bayan da tawagar ta kammala wasannin cikin rukunin farko ba tare da an doke ta ba.

Jamus ce ta daya a rukunin da maki bakwai, sai Switzerland ta biyu da maki biyar, dukkansu biyun sun kai zagayen 'yan 16.

Daya wasan rukunin farko kuwa Hungary ce ta doke Scotland 1-0. kenan Hungary ce ta ukun teburi da maki uku da kuma Scotland mai maki daya ta hudu.

Wasa na uku uku a rukuni na biyu ranar Litinin 24 ga watan Yuni

  • Croatia da Italiya
  • Albania da Sifaniy

Sifaniya. ce ta daya a rukuni na biyu da maki shida sai, Italiya ta biyu da uku da Albani mai maki daya da kuma Croatia itama maki daya ta hudun teburi.

People are also reading