Home Back

SHARI’AR NEMAN CIRE GANDUJE DAGA SHUGABANCIN APC: Kotun Tarayya ta sa ranar fara sauraren ƙorafin shugabannin APC reshen Arewa ta Tsakiya

premiumtimesng.com 2024/7/2
TSUNTSUN DA YA KIRA RUWA: Ko Tinubu zai iya tsamo Ganduje daga ruwan tsomomuwar da ke neman tafiya da shi?

A ranar Alhamis ce Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sa ranar 13 ga Yuni, domin fara sauraren ƙarar da shugabannin APC reshen Arewa ta Tsakiya suka shigar, inda su ke roƙon a cire Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, bisa zargin cewa ba a naɗa shi a bisa halastacciyar hanya ba.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ce a ranar 13 ga Yuni ɓangarorin biyu kowane zai yi wa kotu cikakken bayanin abubuwan da ake inkari a kai.

A cikin ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/599/24, APC Reshen Arewa ta Tsakiya sun garzaya kotu bisa jagorancin Alhaji Saleh Zazzaga daga Jihar Filato, suka maka Ganduje kotu, bisa zargin cewa ya hau shugabancin APC ta ɓarauniyar hanya.

Sun ce ya hau muƙamin a lokacin da haƙƙin Arewa ta Tsakiya ne, aka danne aka bai wa Ganduje, kamar yadda yake a yarjejeniyar jam’iyya.

A cikin ƙarar an haɗa da uwar jam’iyyar APC ta ƙasa da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

Masu shigar da ƙara na roƙon kotu ta umarci INEC ta ƙi karɓar duk wata nasarar da APC ta yi a zaɓukan da ta shiga tun daga ranar 3 ga Agusta, 2023, ranar da aka naɗa Ganduje shugabancin APC.

Sun kuma nemi a soke duk wani zaɓen fidda-gwani ko naɗi da APC ta yi bayan hawan Ganduje shugabancin jam’iyya.

Masu shigar da ƙara sun ce Majalisar Zartaswar APC ta karya dokar APC a naɗin da ta yi wa Ganduje, wanda ɗan Kano ne, shiyyar Arewa maso Yamma, wanda ya maye gurbin Abdullahi Adamu, ɗan Jihar Nasarawa daga Arewa ta Tsakiya.

Sun ce naɗa Ganduje ya saɓa wa Sashe na 31.5(1) na kundin dokokin APC. Tare da cewa doka ta ce idan aka cire shugaban jam’iyya kafin cikar wa’adin sa, to za a maye gurbin sa da ɗan shiyyar wanda aka ce ɗin.

Saboda haka masu shigar da ƙara suka ce kamata ya yi a maye gurbin Adamu da wani daga Arewa ta Tsakiya, ba Ganduje daga Arewa maso Yamma ba.

A ranar Alhamis, lauyan masu ƙara Ayuba Abdul ya shaida wa kotu cewa an yi ƙoƙarin aika wa Ganduje takardar ƙara, amma ba a yi nasara ba. Amma abin mamaki sai ga lauyan Ganduje a ranar ya bayyana a kotu, duk kuwa da cewa bai karɓi kwafen takardun maka Ganduje kotun ba.

People are also reading