Home Back

WATANDAR NAIRA BIKIYAN 3: ICPC ta damƙe wani darakta a Hukumar TETFund

premiumtimesng.com 2024/5/19
Tetfund
Tetfund

Rahoton da PREMIUM TIMES ta buga dangane da yadda aka biya Naira biliyan 3 a kwangilar bogi a Hukumar TETFund, ya zaburas da Hukumar ICPC, har ta damƙe Daraktar Harkokin Kuɗaɗe ta hukumar, Gloria Olotu.

Wasu manyan jami’an ICPC sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an gayyaci Gloria da wasu daraktoci biyu zuwa Ofishin ICPC a ranar Alhamis, domin yi masu tambayoyi, aka ce su koma washegari Juma’a kenan,

Yayin da aka saki Darakta Okunlola da Odo, aka ce su koma washegari, ita kuwa Gloria sai aka damƙe ta, aka tsare.

An ce an tsare ta ne saboda ta kasa cika sharuɗɗan beli, kuma ana yi mata kallon “ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da watandar Naira biliyan 3 ɗin.”

Kakakin Yaɗa Labaran ICPC, Ademola Bakare ya tabbatar wa PREMIUM TIMES tsare Gloria da suka yi a Hedikwatar ICPC.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Hukumar TETFund ta biya Naira biliyan 3 a kwangilar bogi, kwanaki 5 kafin cikar wa’adin mulkin Buhari.

Kwanaki biyar kafin cikar wa’adin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Hukumar Raya Ilmin Manyan Makarantu (TETFund), ta bayar da kwangilar Naira biliyan 3.8, (N3,812,500,000) ba tare da bin ƙa’ida ba.

An kamfaci kuɗaɗen an biya ba tare da an yi kwangilar ba tare da alamar aiwatar da ko kaɗan na kwangilar ba.

PREMIUM TIMES ta bankaɗo yadda TETFund ta biya Naira biliyan 2.9 (2,932,032,516.28) a ranar 30 ga Yuni da 17 ga Nuwamba, 2023.

TETFund ta kamfaci kuɗaɗen daga cikin asusun ayyukan kasafin 2023, waɗanda aka ware domin yin wasu ayyuka a manyan makarantu 251 a cikin faɗin ƙasar nan.

Kuɗaɗen na ayyukan rarar kasafin 2023 ɗin dai Naira biliyan 15.2 ne. Amma maimakon TETFund ta sakar wa makarantun kuɗaɗen, kamar yadda doka ta tanadar, sai hukumar ta cire kaso 50 bisa 100 na kuɗaɗen, daga kowace makaranta. Kuɗi sun tashi Naira biliyan 7.6 kenan.

PREMIUM TIMES ta gano cewa TETFund ba ta buga tandar neman ‘yan kwangilar da za su yi gasar neman kwangilar ba, kamar yadda dokar bayar da kwangiloli ta ƙasa ta tanadar.

Sannan kuma babu amincewar Majalisar Zartaswa ko shi kan sa Shugaban Ƙasa.

TETFund ta bayar da kwangilar bogin ce ga wani kamfani mai suna Fides Et Ratio Academy.

Wannan kamfani dai na gidoga ne, domin ko shafin yanar gizo ba shi da shi a intanet. Amma dai TETFund ta ce “kamfanin Lasisin IP ne mallakar Farfesa Klaus Stierstorfer ne.”

Takardar bayar da kwangilar ta na ɗauke da sa hannun amincewar Daraktan Ayyukan Musamman, Kolopo Akulana.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Hukumar Tantance Haƙiƙanin Adadin Kuɗaɗen Kwangila (BPE), amma ta ce ba ta san da labarin bayar da kwangilar ba, kuma ba a tuntuɓi Ofishin BPE domin ya tantance kuɗaɗen kwangilar kamar yadda doka ta tanadar ba.

An danƙara wa kamfanin da aka ce an bai wa kwangilar Naira 550 a ranar 30 ga Yuni, 2023, a asusun bankin sa na Fedility Bank.

Kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ya amince a tura kuɗaɗen kamar yadda lambar tura kuɗaɗen ta nuna, wato CBN/PROJ/224/JUN2023.

Ranar 12 ga Yuli kuma aka tura Naira miliyan 820, kuma ranar 26 ga Yuli aka tura Naira biliyan 1.5, sai kuma ranar 17 ga Nuwamba aka tura Naira miliyan 62, kuma duk CBN ke tura kuɗaɗen bisa umarni da amincewar TETFund.

TETFund ta yi ƙoƙarin amsa tambayoyin da PREMIUM TIMES ta aika mata dangane da wannan gidogar kwangilar bogi. Amma babu wani cikakken bayanin da zai gamsar, sai inda-inda da kame-kamen neman hujjojin da ba su da ko guda ɗaya.

People are also reading