Home Back

Yan Sanda Sun Kama Ƙasurgumin Ɓarawo a Bauchi, Ya Sace N120m da Kayayyaki Rututu

legit.ng 2024/7/6
  • Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta cafke babban ɓarawo da ake zargin ya fitini al'umma da sace-sace
  • Ɓarawon mai suna Glory Samuel ya sace makudan kudi da kayayyaki na miliyoyin kudi daga mutane da dama a jihar
  • Glory Samuel ya bayyana yadda ya fara shiga sace-sace da hanyoyin da yake bi wajen samun nasara idan ya nufi yin sata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wani babban ɓarawo mai suna Glory Samuel.

Rundunar yan sanda tana zargin Glory Samuel da hannu a satar makudan kudi da kayayyaki da dama.

Bauchi
Yan Sanda sun kama babban barawo a Bauchi. Hoto: Nigeria Police Force Bauchi State Command Asali: Facebook

Legit ta tabbatar da lamarin ne cikin wani sako da rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Glory ya fara sata a Bauchi

Binciken yan sanda ya bayyana cewa Glory ya fara sata ne yayin da ya hadu da wani aboki a kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamantin tarayya a jihar Bauchi.

A cewar Glory, ya hadu da abokin ne a shekarar 2011 kuma shi ya fara nuna masa yadda za su saci kudi ta wayoyin hannun mutane, rahoton Leadership.

Kudin da aka kama 'barawon' da su

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa babban barawon ya wawushewa wani makwabcinsa kudi kimanin N120m a asusun banki.

Sannan kuma yayin da rundunar ta tsananta bincike ta samu wasu kudi kimanin N35,000,000 a tattare da shi.

Kayan da aka kama a hannun Glory

Har ila yau yan sanda sun tabbatar da samun wasu kayan a hannun Glory da suka hada da Keke Napep takwas, gidaje da ba a kammala ba guda biyu.

An samu karin buhunan gawayi 60, buhunan taki 30, babur guda biyu da keken dinki guda biyu duk a hannun Glory Samuel.

Glory yana ikirarin cewa yana harkokin kasuwanci ta yanar gizo ne idan aka tambaye shi game da yadda yake samun kuɗi.

Atiku Abubakar ya yi magana kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana mafita kan yadda yan bindiga suka fara kashe manya a Arewa.

Atiku Abubakar ya yi martani ne bayan da yan bindiga suka kashe mataimakin shugaban jami'ar UDUS da wani Birgediya Janar a Abuja.

Asali: Legit.ng

People are also reading