Home Back

Ko Dakatar Da Harajin Shigo Da Abinci Zai Yi Tasiri?

leadership.ng 2024/8/20
Dawanau

Gwamnatin tarayya ta amince da janye haraji na tsawon kwanaki 150 kan shigo da masara, shinkafa, da alkama, saniya da sauran kayan abinci a wani mataki na yaki da hauhawar farashi da karancin kayayyakin abinci a kasar nan.

Da yake ganawa da ‘yan jarida a Abuja ranar Litinin, ministan gona da wadata kasa da abinci, Sanata Abubakar Kyari ya ce shirin janye harajin ya kunshi hanyoyin kasa da kuma na iyakokin ruwa.

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi duk mai yiyuwa domin tabbatar da kariya da inganci kayan abincin da za a shigo da su daga kasashen ketare.

Ya tabbatar da cewa, gwamnati za ta ci gaba da yin duk mai yiyuwa wajen samar da sauki kan matsin da ake ciki musamman na hauhawar farashi da kuma tabba-tar da kayan da ake shigowa da su na da inganci domin kare lafiyan ‘yan kasa.

“Bugu da kari kan shigo da kayayyakin abinci da kamfanoni masu zaman kansu za su yi, ita ma gwamnatin tarayya za ta shigo da alkama 250,000MT da kuma masara 250,000MT daomin kara wadata kasa da abinci.”

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa, ba a nan gizo ke saka ba, domin kullum al’amura a Nijeriya a kaikaice suke, inda rijiya takan bayar da ruwa gugu ta hana.

A cewrsu, a yanzu dai an ji an saukaka wa ‘yan kasa amma bai zama dole ‘yan kasuwa su sauke farashi ba.

People are also reading