Allahu Akbar: Mahaifiyar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ta Rigamu Gidan Gaskiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Legas - Yanzu muke samun labarin rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Bulola Saraki, watau Madam Florence Morenike Saraki.
Rahotanni sun bayyana cewa, mahaifiyar fitaccen ɗan siyarar ta koma ga mahaliccinta ne tana da shekaru 88 a duniya.
Dakta Abubakar Bukola Saraki ne ya fitar da sanarwar mutuwar mahaifiyarsa, Cif Misis Florence Saraki a shafinsa na X a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Bukola Saraki ya ce:
"Cikin bakin ciki da mika lamura ga Allah, ina sanar da rasuwar mahaifiyata, Cif Misis Florence Morenike Saraki, wadda ta rasu a yau Talata, 18 ga watan Yunin 2024."
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce nan gaba kaɗan za su sanar da bayani na lokacin jana'izar mamaciyar tare da godiya ga wadanda suka yi masu ta'aziyya.
Kalli sanarwar a nan ƙasa:
A hannu daya, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa marigayiyar ta fada doguwar suma ne kafin a garzaya da ita wani asibitin jihar Legas kan ciwon da ya shafi tsufa.
Wasu daga cikin ‘ya’yan masarautar Saraki da suka so a sakaya sunansu sun tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a garin Ilorin a daren jiya.
Marigayi Florence ita ce matar Olusola Saraki, wande ya kasance sanata a Jamhuriyar Najeriya ta biyu kuma jigon siyasa a jihar Kwara har zuwa rasuwarsa a shekarar 2012.
Asali: Legit.ng