Home Back

Edo: Jam'iyyar PDP Ta Gamu da Babbar Matsala Ana Shirin Zaɓen Gwamna

legit.ng 2024/6/30
  • Ɗan takarar gwamnan jihar Edo karƙashin inuwar jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo ya samu cikas a kwamitin yakin neman zaɓensa
  • Mamban kwamitin kamfen Ighodalo, Felix Isuku ya fice daga jam'iyyar PDP saboda rikicin cikin gida da ya kawo rabuwar kai
  • Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan PDP ta kori tsohon mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu da wasu kusoshi biyu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Wani mamba a kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Edo, Prince Felix Isuku, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Babban jigon ya kuma fice daga jam'iyyar PDP yayin da harkokin kamfe suka kankama domin tunkarar zaɓen gwamnan Edo wanda za a yi ranar 21 ga watan Satumba 2024.

Dan takarar gwamnan PDP a Edo, Asue Ighodalo.
Jam'iyyar PDP ta rasa mamban kwamitin yakin zaɓen gwamna a jihar Edo Hoto: Asue Ighodalo Asali: Facebook

Prince Isuku ya bar PDP ne sa'o'i 48 bayan kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ta jihar Edo ya kori tsohon mataimakin gwamna, Philip Shaibu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Punch ta tattaro, bayan Shaibu NWC karƙashin jagorancin shugaban PDP na jiha, Tony Aziegbemi, ya kori tsohon ɗan majalisar tarayya, Omoregie Ogbeide-Ihama.

Mstaimakin shugaban PDP na shiyyar Kudu maso Kudu, Dan Orbih, shi ne cikon mutim na uku da jam'iyyar ta kora bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.

Kwana biyu bayan haka, Price Isuku, mamban kwamitin kamfen ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Asue Ighodalo, ya fice daga jam'iyyar.

Ya sanar da haka ne a wata takarda da ya aika wa shugaban jam'iyya na jiha da sakatare da shugaɓan jam'iyyar na gunduma ta 4 a ƙaramar hukumar Owan ta Gabas.

Ya alaƙanta dalilinsa na barin PDP da rigingimun cikin gida waɗanda suka kai ga rarrabuwar kan da ba a taɓa ganin irinsa ba a jam'iyyar.

A rahoton Daily Post, ɗan siyasar ya ce:

"Na rubuto wannan takarda domin sanar da ku cewa bayan tattaunawa mai zurfi da abokanaina na siyasa a mazabar Owan ta Gabas/Yamma na yanke shawarar ficewa daga PDP.”

Yahaya Bello ya ɓuya a Kogi

A wani rahoton kun ji cewa Jigon PDP ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamna Yahaya Bello na cikin gidan gwamnatin jihar Kogi yana samun kariya daga Ahmed Ododo.

Austin Okai, tsohon ɗan takarar majalisar tarayya ya faɗi haka ne yayin da EFCC ke ci gaba da koƙarin gurfanar da tsohon gwamnan a kotu.

Asali: Legit.ng

People are also reading