Home Back

Ana Tsaka Da Rikicin Sarautar Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II Ya Yi Nadin Farko

legit.ng 2024/6/29
  • Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi nadin sarauta na farko tun bayan nada shi sarauta da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi a makon da ya gabata
  • Nadin na zuwa ne duk da dambarwar da ta dabaibaye masarautar, yayin da sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya ki amincewa da tsige rawaninsa da gwamnatin jiha ta yi
  • Sarki Sanusi II ya nada Hamisu Mazugal a matsayin mai unguwar Mazugal dake karamar hukumar Dala, daga nan kuma ya ci gaba da karbar caffa da mubaya daga talakawansa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Yayin da sarautar Kano ke kasa tana dabo, Sarkin masarautar jihar na 16, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi nadin mukami. Sarki Sanusi ya nada mai unguwar Mazugal, Hamisu Sani a karamar hukumar Dala.

Muhammadu Sanusi II
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya yi nadin sarauta Hoto: @SanusiLamidoS Asali: Twitter

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi nadi

Vanguard News ta wallafa cewa wannan shi ne nadin sarauta na farko da Malam Muhammadu Sanusi ya yi tun bayan nada shi da gwamnatin Kano ta yi. Sarkin ya hori sabon mai unguwar da ya tabbata ya yi adalci tsakanin talakawansa, tare da bayar da na shi kason wajen gina kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki Sanusi II ya karbi caffa

Yayin da har yanzu Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ki amincewa da tube rawaninsa da gwamnati ta yi, al'umma sun mayar da hankali wajen kai wa Sarki Sanusi II caffa ta ban girma. Hakimai, da kungiyoyin addini irinsu kungiyar 'yan Tijjaniya, da ta 'yan kasuwar kantin kwari da na singer ne suka kai wa sarkin ziyarar mubaya'a, kamar yadda Naija News ta wallafa.

Wanene Sarki tsakanin Sanusi da Aminu?

Har yanzu tirka-tirkar sarautar Kano na daukar hankali, inda a yanzu haka ake da sarakuna biyu a jihar. Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsige na zaune a gidan sarauta na Nassarawa, shi kuma nadadden sarki Muhammadu Sanusi II na fadar sarki dake kofar kudu.

Gwamna Abba ya gana da Nuhu Ribadu

A baya mun kawo muku labarin cewa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ziyarci mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Ya kai ziyarar ne yayin da ake ci gaba da jan daga kan sarautar Kano, har gwamnatin jihar ta yi zargin Ribadu na da hannu wajen dawo da Sarki Aminu Ado Bayero Kano.

Asali: Legit.ng

People are also reading