Home Back

Majalisar Dattawa Ta Gafartawa Sanata Abdul Ningi, Ta Fadi Matakin Gaba

legit.ng 2024/6/28
  • Majalisar Dattawa ta yi zama kan Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi inda ta dauki matakin yi masa afuwa
  • Majalisar ta bayyana amfanin Ningi da kuma kwarewarsa tare da gudunmawar da yake bayarwa maras misaltuwa
  • Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ce matakin da suka dauka na dawo da Ningi ya wuce maganar kabilanci ko addini

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa a Najeriya ta yi wa Sanata Abdul Ningi afuwa bayan dakatar da shi tsawon watanni uku.

Majalisar ta kuma bukaci sanatan ya dawo bakin aiki bayan dakatar da shi a ranar 12 ga watan Maris din wannan shekara.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar, Sanata Abba Moro shi ya gabatar da haka a yau Talata 28 ga watan Mayu, cewar Channels TV.

Moro ya ce dakatar da Abdul Ningi abin takaici ne inda ya ce ya dauki nauyin dukkan abin da sanatan ya aikata.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya bayyana irin amfanin Ningi da gudunmawar da ya ke bayarwa saboda kwarewarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya de matakin dawo da Ningi ya wuce maganar addini ko kabilanci inda ya kara jaddada himmatuwar majalisar wurin hadin kan yan kasa.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading