Home Back

“Yadda Tinubu da Jihohi Za Su Samu Kudin Biyan Sabon Albashin Ma’aikata,” in Ji Falana

legit.ng 2024/7/1
  • A ranar Alhamis ne Femi Falana ya dage kan cewa gwamnatin tarayya da na jihohi za su iya biyan mafi karancin albashi
  • Babban lauyan ya nemi Shugaba Tinubu da jihohi da su yi amfani da kudin sata da aka kwato domin biyan sabon albashi
  • Har yanzu dai ma’aikata da gwamnati ba su cimma matsaya kan sabon albashin ba inda 'yan kwadago suka ki karbar tayin N62,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Lauyan kare hakkin bil’adama, Femi Falana (SAN) ya ba gwamnatin tarayya da jihohi za shawarar hanyar da za su bi domin su iya biyan sabon mafi karancin albashi.

Babban lauyan ya nemi Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin jihohi da su yi amfani da kudin sata da aka kwato domin biyan sabon albashin ma'aikatan.

Femi Falana ya yi magana kan sabon albashin ma’aikata
Femi Falana ya ba Tinubu da jihohi shawara kan sabon mafi karancin albashi. @Imranmuhdz, @officialABAT Asali: UGC

Femi Falana ya ba da wannan shawar ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a daren ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Falana ya ba Tinubu da jihohi shawara

Babban lauyan ya bukaci hukumomin Najeriya da su yi amfani da karfin ikon siyasa domin biyan mafi karancin albashi da kungiyar kwadago ke bukata.

A cewar Falana:

“Gwamnatocin jihohin da ke cewa ba su da kudin da za su iya biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi tatsuniya kawai suke yi, kudin na nan a kasa.
"Abin da kawai za su yi, ciki har da gwamnatin tarayya, shi ne a yi amfani da karfin ikon siyasa domin fito da kudin sata da aka kwato, wadanda ke a lalitar gwamnatin tarayya.”

Ana kan takaddamar mafi karancin albashi

Har yanzu dai hadaddiyar kungiyar kwadago da gwamnatin Najeriya suna kan yin takun-saka kan sabon mafi karancin albashin ma'aikatan kasar.

A wani taro da aka yi a ranar Juma’a a Abuja, kungiyar kwadago ta rage bukatarta zuwa N250,000 daga N494,000, yayin da gwamnatin tarayya ta kara tayi daga N60,000 zuwa N62,000.

ALGON ta maganku kan sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar kananan kukumomin Najeriya (ALGON) ta ce zai yi wahala kananan hukumomi su iya biyan N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Kungiyar ALGON ta ce da yawan kananan hukumomi ba sa iya biyan N30,000 da aka amince da shi a 2019 balle a yi maganar N62,000.

Asali: Legit.ng

People are also reading