Home Back

Kano: Duk da Umarnin Kotu da Ke Neman Daƙile Sanusi II, Gwarzo Ya Gana da Sarkin a Fadarsa

legit.ng 2024/7/2
  • Mataimakin gwamnan jihar Kano, Abdulsalam Aminu Gwarzo ya kai ziyara fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II a fadarsa
  • Gwarzo ya kai ziyarar a yau Laraba 29 ga watan Mayu duk da umarnin Babbar Kotun Tarayya kan kujerar Sanusi II a yanzu
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dmabarwa kan sarautar jihar Kano da ya ki ci ya ki cinyewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautun Kano, mataimakin gwamna jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ziyarci Muhammadu Sanusi II.

Gwarzo ya kai ziyarar duk da umarnin Babbar Kotun Tarayya kan tuge sabon sarkin daga karagar sarauta a jihar.

A cikin faifan bidiyon da aka yada a shafin X, an gano Gwarzo da tawagarsa suna shiga cikin fadar a yau Laraba 29 ga watan Mayu.

Sai dai babu karin bayani kan abin da suka tattauna amma hakan bai rasa nasaba da yin mubaya'a ko goyon baya ga Sarkin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musabbabin rikicin sarautar Kano

An shiga rikicin sarauta a Kano tun bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga kan karaga.

Gwamnan Abba Kabir shi ya sauke Aminu Ado bayan sanya hannu a sabuwar dokar Majalisar jihar.

A makon da ya gabata ne Majalisar ta amince da rushe masarautu guda biyar da gwamnan Abdullahi Ganduje ta kirkiro a shekarar 2019.

Lauya ya magantu kan rikicin sarautar Kano

A wani labarin, wani lauya a Najeriya, Wale Adeagbo ya yi martani kan rikicin sarautar jihar Kano da ke faruwa a yanzu.

Lauyan ya koka kan yadda kotuna ke ba da umarni masu cin karo da juna kan matsalar sarautar jihar.

Sai dai ya ce a tsarin doka babu inda aka tabbatar cewa Babbar Kotun Tarayya ta fi Babbar Kotun jiha iko.

Asali: Legit.ng

People are also reading