Home Back

HAJJIN BANA; Gwamna Balan Bauchi ya gwangwaje maniyyatan jihar da kwautar dala 100 kowannensu ƙarin guziri

premiumtimesng.com 2024/9/27
Ina nan kan baka ta: A rika ba masu fama da Coronavirus ‘Chloroquine da Zithromax’ – Gwamnan Bala
Bala Kauran Bauchi

Gwamnan jihar Bala Mohammed ya baiwa daukacin alhazan jihar Bauchi 2,682 da ake shirin jigilar su zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana dala 100 kowannen su, ƙarin kuɗin guziri.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga maniyyatan a wani taron bankwana da aka yi a sansanin Hajji na Sultan Sa’ad Abubakar ranar Alhamis.

Bala Mohammed ya kuma yi amfani da wannan damar wajen kaddamar da jigilar maniyyata alhazai 2,682 zuwa Saudiyya, inda ya bukace su da su zama jakadun jihar a lokacin da suke kasa mai tsarki.

Bayan haka ya ce gwamnatin Bauchi ta yi wa Alhazan jihar kyakkyawar shiri domin su sauke faralinsu cikin yanayi mai sauƙi ba tare da sun wahala ba.

Ua kara da cewa gwamnati ta aika da kwararrun likitoci, malamai da za su rika yi wa mutane nasiha da jagora da kuma sauran abubuwan da za su buƙata.

People are also reading