Jigon APC, Salihu Lukman Ya Nakasa Jamiyyar Bayan Ya Yi Murabus, Ya Jero Dalillai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban APC a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya yi murabus.
Lukman ya zargi jamiyyar da rashin iya shugabanci da kuma munanan tsare-tsare wanda ya jefa kasar a halin kunci.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yau Laraba 12 ga watan Yuni a Abuja, cewar The Nation.
Tsohon darakta-janar na kungiyar gwamnonin bai fadi matakin da zai dauka na gaba ko jam'iyyar da zai koma ba.
Sai dai Lukman ya ce ya hada kai da wasu manyan shugabannin siyasa domin tunkarar zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng