"Kowa Ya Yi Abin da Zai Iya": Kungiyar Gwamnoni Ta Fitar da Matsaya Kan Karin Albashi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - Kungiyar gwamnonin Kudancin Najeriya ta yi zama na musamman kan mafi karancin albashi da ake tababa a kai.
Kungiyar ya bukaci ba kowace jiha damar biyan mafi karancin albashin abin da za ta iya duba da halin da ake ciki, cewar Daily Trust.
Hakan ya biyo bayan matakin kungiyar kan mafi karancin albashi a ganawar da ta yi yi a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce duba da halin da ake ciki, kamata ya yi kowane gwamna ya tattauna da kungiyar NLC reshen jiharsa domin samun mafita
Gwamnoni sun kuma bukaci a ba su damar kula da albarkatun kasa da suke da shi a jihohinsu ba tare da katsalandan ba.
Suka ce ba da lasisin masu hakar ma'adinai ba tare da sanya gwmanonin ba shi ke kara rashin tsaro a jihohi da dama.
Wannan mataki na gwamnonin na zuwa ne yayin da mataimakin shugaban kasa ya shiga wata ganawa da gwamanonin Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya shiga wata ganawa ta musamman da gwamnonin Najeriya.
Ganawar ba ta rasa nasaba da maganar mafi karancin albashi da ake tababa a kai cikin ƴan kwanakin nan da muke cikin.
Asali: Legit.ng