Home Back

Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Jawo Yawaitar Ayyukan Ta'addanci a Afirika

legit.ng 2024/5/18

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan yawaitar ayyukan ta'addanci da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a nahiyar Afirika.

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa kuɗaɗen da ake samowa daga ƙasashen waje su ne suka ƙara iza wutar matsalolin guda biyu da ake fama da su.

Tinubu ya magantu kan ta'addanci a Afirika
Tinubu ya bude taro kan yaki da ta'addanci a Afirika Hoto: @DOlusegun Asali: Twitter

Ya yi kira ga ƙasashen duniya da su taimaki nahiyar Afirika shawo kan matsalar saboda sun bada gudunmawa wajen samar da ita.

Shugaba Tinubu ya kuma nuna muhimmancin buƙatar ƙasashen Afirika su ƙara ƙarfafa haɗin kai a tsakaninsu domin magance barazanar da ta'addanci ya ke yi wa nahiyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasan ya yi magana ne a ranar Litinin a wajen buɗe taro na kwana biyu kan magance ta'addanci a nahiyar Afirika, wanda ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya shirya a Abuja.

Jawabin na Tinubu na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokim yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a shafin X.

Tinubu ya yi nuni da cewa kuɗaɗen da ake shigowa da su daga wasu wuraren ne ke ƙara iza wutar haƙo ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba wanda ya rikiɗe ya zama ɗaukar nauyin ta'addanci.

A cewarsa haƙo ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba yanzu ya koma hannun ƴan ta'adda domin samun kuɗaɗe daga ƙasashen waje waɗanda suke amfani da su wajen siyan makamai.

Asali: Legit.ng

People are also reading