Home Back

‘Sarkin Yawa Ya Fi Sarkin Ƙarfi’, Tinubu ya jinjina wa Ƴan gwagwarmayar tabbatar da dimokraɗiyya a Najeriya

premiumtimesng.com 2024/7/2
‘Sarkin Yawa Ya Fi Sarkin Ƙarfi’, Tinubu ya jinjina wa Ƴan gwagwarmayar tabbatar da dimokraɗiyya a Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya jinjina wa gwarazan da suka shafe shekaru suna gwagwarmayar tabbatar da dimokraɗiyya a Najeriya.

A cikin jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya, Tinubu ya bayyana cewa jajircewar da waɗannan gwaraza suka yi ne ya kai mu ga inda dimokraɗiyyar Najeriya ta ke a yanzu.

Ya jinjina masu kan irin dauriya da juriyar gwagwagwa da suka riƙa yi da sojojin mulki, har ta kai an ɗaure wasu, wasu sun rasa rayukan su, wasu kuma suka yi hijira suka har ƙasar.

” A cikin wannan gwagwarmayar, mun rasa rayukan gwaraza maza da mata. Ciki kuwa har da wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa 12 ga Yuni, 1993, kuma ya zamo tambarin dimokraɗiyya, wato Cif MKO Abiola, da mai ɗakin sa Hajiya Kudirat da sauran wasu gwarazan irin su Janar Shehu Musa ‘Yar Adua da Pa Afred Rewane, duka sun sadaukar da rayuwar su wajen samar wa Najeriya makoma mafi dacewa.

“Mu yi jinjinar ban-girma ga mutanen da ba za a manta da su ba, irin su, Cif Anthony Enahoro da Chif Abraham Adesanya da Kwamanda Dan Suleiman da Cif Arthur Nwankwo da Cif Chukwuemeka Ezeife da Admiral Ndubuisi Kanu da Cif Frank Kokori da Cif Bola Ige da Cif Adekunle Ajasin da Cif Ganiwu Dawodu da Cif Ayo Fasanni da Cif Gani Fawehinmi da Cif Olabiyi Durojaiye da Dakta Beko Ransome-Kuti da Chima Ubani da dai sauransu da suka riga mu gidan gaskiya.

” Zai zama an yi tuya an mance da albasa idan aka manta da sadaukawar gwaraza irin su Alani Akinrinade da farfesa Bolaji Akinyemi da Farfesa Wole Soyinka da Cif Ralph Obioha da Cif Cornelius Adebayo ba, da dai sauran su, mutane ne da suka jure wa raɗaɗi da wahalhalun rayuwar ‘yan gudun hijira.

“A yayin da gwarazan ‘yan gudun hijirar ke aiki daga nesa don tabbatar da diga-digin dimokraɗiyya, takwaroroin su da ke gida Najeriya sun ci gaba da nuna juriya ga matsin mulkin sojoji. Cikin su akwai Olisa Agbakoba da Femi Falana da Abdul Oroh da Sanata Shehu Sani da Gwamna Uba Sani da Cif Olu Falae da sauran jagororin tabbatar da ganin cewa an samar da demokradiyya, irin su Cif Ayo Adebanjo da Cif Ayo Opadokun.

People are also reading