Home Back

Shugaban PDP Ya Zargi APC da Kokarin Kawo Rabuwar Kawuna a Jam'iyyar Adawa

legit.ng 2024/5/2

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Ambassada Umar Iliya Damagum, ya yi zargin cewa jam'iyyar APC na son rarraba kawuna a jam'iyyar adawan.

Iliya Damagum ya bayyana hakan ne a wajen taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na jam'iyyar PDP a birnin tarayya Abuja.

Shugaban PDP ya zargi APC
Iliya Damagum na zargin APC da kokarin kawo rudani a jam'iyyar adawan Hoto: PDP Update Asali: Twitter

Muƙaddashin shugaban na PDP ya kuma zargi gwamnatin APC da jefa ƙasar nan cikin halin wuya, cewar rahoton jaridar Tribune.

Ya gayawa mambobin jam'iyyar cewa ya kamata su fahimci cewa ƴan Najeriya na jiran su zo su ceto ƙasar nan daga halin da ta tsinci kanta a ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kira da a kafa kwamiti mai ƙarfi wanda zai sulhunta ƴaƴan jam'iyyar waɗanda ba sa ga maciji da juna.

"Akwai buƙatar a kafa kwamitin sulhu mai ƙarfi wanda zai haɗa kan fusatattun mambobinmu, musamman waɗanda suka samu saɓani a lokacin zaɓen fidda gwani da ya gabata. Har yanzu ba a makara ba."
"Dole ne mu sake fasali da ƙarfafa jam'iyyar domin yin adawa mai ma'ana wacce za ta kawo sababbin tsare-tsare wajen gudanar da mulkin ƙasar nan."
"Dole ne mu fahimci cewa ƴan Najeriya na son PDP kuma suna jiran da mu kawo musu ɗauki kan wahalhalun da APC ta jefa su a ciki."

- Ambassada Umar Iliya Damagum

Asali: Legit.ng

People are also reading