Home Back

Man City za ta fara Premier League da Chelsea a 2024/25

bbc.com 2024/7/6
Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City za ta fara da ziyartar Chelsea a wasan makon farko a Premier League kakar 2024/25.

Ita kuwa Ipswich Town daya daga cikin sabbi ukun da za su buga babbar gasar tamaula ta Ingila a bana, za ta fara da karbar bakuncin Liverpool.

Wannan shi ne karon farko da Ipswich za ta kara a Premier League tun bayan shekara 22, wadda za ta yi wasan farko ranar 17 ga watan Agustan 2024.

To sai dai za a fara da bude labulen gasar da wasa tsakanin Manchester United da Fulham a Old Trafford ranar Juma'a 16 ga watan Agusta.

Arsenal, wadda ta yi ta biyu a gasar da aka kammala za ta karbi bakuncin Wolverhampton a Emirates ranar Asabar, yayin da Aston Villa za ta je West Ham.

Southampton wadda ta koma buga Premier League, bayan kaka daya a Championship za ta fafata da Newcastle a St James' Park.

Everton za ta karbi bakuncin Brighton da fafatawa tsakanin Nottingham Forest da Bournemouth a gumurzun ranar Asabar.

Akwai karin labarai...

People are also reading