Home Back

Gwamnatin Kano Ta Harzuƙa Ƴan Jarida, Sun Dauƙi Mataki Kan Abba da Jami’ansa

legit.ng 2024/7/7
  • Biyo bayan taron gaggawa da ta yi a yau Litinin, kungiyar 'yan jaridu masu aiko da rahoto sun janye aiki daga gwamnatin Kano
  • Kungiyar ta haramta wa mambobinta yaɗa duk wani aiki da ya shafi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da ma'aikatun jihar baki daya
  • Shugaban ƙungiyar, Aminu Garko ya yi nuni da cewa 'yan jaridunta na fuskantar barazana da hantara a yayin gudanar da ayyukansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Kungiyar 'yan jaridu masu aiko da rahotanni da ke karkashin kungiyar 'yan jaridar ta kasa (NUJ) ta sanar da kauracewa duk wasu ayyukan da suka shafi gwamnatin jihar Kano.

Wannan matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa na kungiyar da shugabanta Aminu Ahmed Garko ya jagoranta a ranar Litinin.

Gidan gwamnatin jihar Kano
'Yan jarida sun dakatar da yada rahoton ayyukan gwamnatin Kano. Hoto: @Kyusufabba Asali: Twitter

Kungiyar 'yan jaridu masu kawo rahoton sun yi wannan taron ne saboda cin kashin da ake yi masu a gidan gwamnati da hukumomin gwamnati a jihar, in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A duk lokacin da mambobinta suka ne dauko rahoto da ya shafi gwamnati da jami'anta, suna fuskantar hantara, a cewar kungiyar.

"Ana cin zarafin 'yan jarida a Kano" - Garko

Shugaban ƙungiyar ya ce:

"Duk da tarin korafe korafe da muka yi da kuma kokarin tattaunawa da gwamnati da jami'anta domin shawo kan matsalar, amma babu wani sauyi da aka samu.
"Mambobin kungiyar mu na fuskantar cin fuska, hantara da kyara, wasu lokutan ma bar da cin zarafi yayin gudanar da ayyukan su."

Aminu Garko ya ce abin baƙin ciki ne ace gwamnatin jihar ta fifita bara gurbin masu kawo rahoto a kan kwararrun 'yan jarida.

Kano: 'Yan jarida sun janye aiki

Kungiyar ta yanke hukunci cewa:

"Dangane da hakan, muna bakin cikin sanar da ku cewa ba za mu sake daukar rahoton duk wani taro, sanarwar gwamnatin jihar ko yin hira da wani jami'in gwamnati ba.
"Za mu zuba idanu mu ga matakin da gwamnatin jihar za ta dauka, idan ta ba mu tabbacin na kare martabar ma'aikatan mu, to za mu dawo bakin aiki."

Kungiyar ta yi kira ga dukkanin 'yan jarida da ke karkashin ta da su yi biyayya ga wannan umarni tare da mara mata baya wajen yaƙi da cin zarafin 'yan jarida a Kano.

Abba ya kaddamar da ginin tituna

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin gina tituna biyu a garuruwan daban daban da za su lakumne Naira biliyan 2.6.

Wannan na daga shirin gwamnatin Kano na gina titunan karkara a garuruwa 10 da ke mazabun tarayya uku na jihar in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

People are also reading