Katsina: Ƴan Bindiga Sun Farmaki GRA, Sun Sace Farfesa Da Wani Lakcara a Jami'ar Tarayya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da lakcarori a Jami'ar Tarayya da ke Duntsinma a jihar Katsina.
Miyagun sun sace lakcarori biyu tare da wani mutum guda da safiyar ranar Litinin 3 ga watan Yuni a jihar.
The Guardian ta tattaro cewa maharan sun sace Farfesa Richard Kyaram da ɗansa mai suna Solomon da kuma wani Dakta Hamza.
Wadanda aka sacen suna rayuwa ne a yankin GRA da ke Dutsinma inda maharan suka farmaki yankin da muggan makamai.
Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan sun bi gida-gida inda suke kwacen waya da kudi da sauran kayayyaki masu amfani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Daga bisani an fitar da wadanda aka sacen daga gidajensu inda aka tafi da su wani wuri da ba a sani ba."
- Cewar majiyar
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng