Home Back

Tangalashi da Yamalash: 'Yan jarida masu sharhin wasanni da Hausa

bbc.com 2024/6/30

Tangalashi da Yamalash: 'Yan jarida masu sharhin wasanni da Hausa

Mintuna 3 da suka wuce

'Yan jaridar 'yan asalin jihar Kano sun ce sun jima suna harkar sharhin wasanni a harshen Hausa, ɗaya daga cikinsu Isma'l Abba da aka fi sani da Tangalashi ya ce ya fara ne da wasan ƙwallon dawaki watau Polo.

A nasa ɓangare Abubakar Isa Dandago da aka fi sani da Yamalash ya ce kalmomin da yake amfani da su a lokacin sharhi, zuwar masa suke yi tamkar wahayi a lokacin da yake tsaka da yin sharhin wasannin.

Tangalashi ya ce tun yana ƙarami yake da sha'awar wasanni, kasancewa mahaifinsa ya buga wasanni har zuwa babban mataki, kamar yadda ya bayyana.

People are also reading