Home Back

Qatar na fargaba kan Isra'ila game da yarjejeniyar Gaza

dw.com 2024/7/5
Kakakin ma'aikatar harkokin weajen Qatar Majed al-Ansari
Kakakin ma'aikatar harkokin weajen Qatar Majed al-Ansari

Da ya ke magana a gaban manema labarai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari, ya ce har yanzu kasar ba ta samu wani tabbaci amincewa da sabuwar yarjejeniyar tsagaita buda wutar ba daga Isra'ila.

inda ya ce "Har yanzu muna jiran matsayar Isra'ila kan shawarwarin da Shugaba Biden ya gabatar, mun ga sanarwar da ta saba wa hakan daga bangaren ministan Isra'ila, wannan kuma ba ya bayar da tabbacin cewa Isra'ila za ta karbi yarjejeniyar sulhun."

Kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ke fafatukar ganin bangarorin biyu da ke batakashi sun kai ga amincewa da dakatar da yaki domin kulla wata yarjejeniyar da za ta kai ga samar da zaman lafiya a yankin Gaza da farmakin Isra'ila ya daidaita.

People are also reading