Home Back

MU KOMA GONA: Gwamna Raɗɗa ya maida ma’aikata 722 na ƙananan hukumomi zuwa jami’an aikin gona

premiumtimesng.com 2024/4/27
Manoman Najeriya sun koka game da yunkurin gwamnati na fesa wa farin dango maganin naira bilyan 13.9
Farming

Gwamnatin Jihar Katsina ta maida ma’aikatan ƙananan hukumomi su 732 zuwa jami’an wayar da kan manoma dabarun bunƙasa harkokin noma a jihar.

Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa ne ya bayyana haka, yayin jawabi wurin taron horas da jami’an na kwanaki biyu, ranar Talata a Katsina.

Ya ce gwamnati ta yi wannan dabarar ce domin magance ƙarancin ma’aikatan kula da dabarun noma, kuma ya ƙara da cewa cikin watan Mayu 2023 gwamnatin jihar na da ma’aikatan gona 72 kaɗai.

Gwamnan ya ci gaba da cewa wannan sabon tsarin zai tabbatar da an ɗauko ma’aikaci biyu daga kowace mazaɓa, daga cikin mazaɓu 361 da ke Jihar Katsina.

Ya ce hakan zai sa kenan kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomin jihar 34, za ta sami jami’an harkokin bunƙasa noma biyu kenan.

“Na yi amanna cewa samun waɗannan jami’an inganta harkokin noma zai ƙara inganta noma a jihar nan, ” cewar Raɗɗa, kuma ya ƙara cewa kyakkyawan shiri ne da zai ƙara samar da yalwar abinci ga al’ummar jihar.

“Za a ba su horo dangane da sanin makamar aiki a shiyyoyin sanata a yankin sanatoci uku na jihar. Domin haka zai sa a tabbatar sun ƙware sosai a fannin horon da za a yi masu.”

Raɗɗa ya tabbatar wa manoman jihar Katsina cewa gwamnatin sa za ta sama masu nagartaccen iri da kayan noman bunƙasa yawa da yalwar kayan abinci.

A jawabin sa, Kwanishinan Harkokin Noma na Bunƙasa Kiwo na Jihar Katsina, Ahmed Bakori, cewa ya yi gwamnati ta himmatu wajen bunƙasa harkokin noma, domin a samu wadatar isasshen abinci, kuma a magance matsalar tsaro a jihar Katsina.

 
People are also reading