Home Back

Tinubu ya sa hannu kan dokar musamman, wadda za ta magance tsadar magunguna da wasu kayan kula da marasa lafiya

premiumtimesng.com 2 days ago
Tinubu ya rattaba hannu kan sabon kudirin ba da lamuni na dalibai

LA ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na inganta fannin kiwon lafiya, Shugaba Bola Tinubu ya sa hannu kan dokar musamman, wadda za ta bunƙasa haɗa magunguna da wasu kayan kula da lafiya domin a rage tsadar farashin su.

A ta bakin Ministan Harkokin Lafiya, Pate, ya ce daga cikin magunguna da kayayyakin da za a riƙa haɗawa a nan Najeriya sun haɗa da magunguna, kayan duba maras lafiya, allurai, sirinji da kayan kula da lafiya irin su tawul, mayafai da sauran su.

Wannan sabuwar doka kamar Muhammad Pate ya bayyana, ya ce ba za a riƙa ɗora wa masu masana’antun da ke samar da waɗannan kayayyaki haraji ba, haka ba za su biya harajin Kwastan ko na Harajin Jiki Magayi kan wasu kayan haɗin da suke shigowa dasu daga waje ba

A farkon watan Mayu ne Minista Pate ya bayyana cewa, faɗuwar darajar Naira ya haifar da tsada da hauhawar farashin magunguna

Ministan Kiwon Lafiya da Walwalar Jama’a, Umar Pate, ya danganta tsadar magunguna da hauhawar farashin su, cewa faɗuwar darajar Naira ce ta haifar da hakan a Najeriya.

Pate ya bayyana haka a ranar Talata, tare da cewa faɗuwar darajar Naira na shafar masu masana’antun haɗa magunguna, saboda ba su iya sawo sinadaran haɗa magungunan da sauran kayan haɗi, domin haɗa magunguna a Najeriya.

A taron wanda gidan Talabijin na Channels ya shirya a intanet, an yi shi ne domin murnar cikar talbijin ɗin shekaru 10 da kafuwa.

Sauran matsalolin da ke haddasa tsadar magunguna a Najeriya, a ta bakin Minista Pate, sun haɗa da tsadar kuɗaɗen lodi, jigila da safarar maganin, tsadar kayan inganta fasaha da kuma ƙa’idojin da ke tattare da harkokin haɗa magunguna.

Shugaban taron kuma tsohon Ministan Lafiya, Julius Adelusi-Adewuyi, ya jaddada muhimmancin bunƙasa masana’antun haɗa magunguna a ƙasar nan, sai kuma ƙara narka kuɗaɗe a harkokin haɗa magunguna.

Ita ma Shugabar Daraktar NAFDAC, Moji Adeyeye, ta bayyana cewa hanyoyin da za a bi domin daƙile matsalar ficewar da manyan kamfanonin haɗa magunguna ke yi daga ƙasar nan, su ne a samu ƙarin masana’antu a cikin gida waɗanda za su riƙa haɗa magunguna.

“Saboda muna buƙatar darajar Naira ta tsaya da ƙafafuwan ta a kasuwar musayar kuɗaɗe. Amma babu abin da kamfanonin waje za su haɗa wanda mu na mu na cikin gida ba za su iya haɗawa ba.

“Abin shaƙar iska na ‘inhaler’ ne kaɗai ba za a iya haɗawa a Najeriya ba,” inji ta.

Pate ya ce masu inshorar lafiya a Najeriya ba su kai kashi 10 bisa 100 ba. Ya ƙara da cewa batun inshorar kiwon lafiya a Najeriya ya daɗe ya na fuskantar ƙalubalen rashin wadatattun kuɗaɗe daga gwamnati, tsawon shekaru 40.

“Da yawan mu za mu afka cikin talauci da ƙarewar dukiyoyin mu idan munanan cutuka irin kansa ko ciwon ƙoda suka kama mu, saboda babu da tsarin inshorar lafiya.” Inji Minista.

People are also reading