Home Back

NLC: Rigima Ta Ɓarke Tsakanin Ƴan Kwadago Yayin da Ake Tsaka da Batun Ƙarin Albashi

legit.ng 2024/8/21
  • Rigama ta ɓalle a tsakanin ƴan kwadago yayin da mutum biyu suka fara ikirarin shugabancin ƙungiyar NLC reshen jihar Ondo
  • Wasu ƙungiyoyin ma'aikata 12 sun zaɓi Kwamared Olapade Ademola a matsayin sabon shugaban NLC ta jihar bisa hujjar cewa tsohon shugaban ya yi ritaya
  • Sai dai Kwamared Victor Amoko ya mayar da martanin cewa yana nan daram a matsayin shugaba domin bai yi ritaya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Rikici ya barke a kungiyar kwadago NLC reshen jihar Ondo yayin da mutane biyu ke ikirarin shugabancin ƙungiyar.

NLC reshen jihar Ondo ta dare gida biyu ne a daidai lokacin da Kwamared Victor Amoko da Kwamared Olapade Ademola ke fafutukar neman shugabanci.

Yan kwadago.
Kungiyar NLC ta shiga matsala, shugabanni biyu sun bayyana a Ondo Hoto: Nigeria Labour Congress HQ Asali: Twitter

Daily Trust ta ce an zabi Ademola a matsayin shugaban kungiyar a wani taro na musamman da majalisar zartarwar NLC ta jihar (SEC) ta gudanar ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron da aka zaɓi Ademola ya samu halartar kungiyoyi 22 kuma mataimakin shugaban kungiyar NLC, Kwamared Busola Adewumi ne ya jagoranta.

Sai dai mambobin kungiyar malamai ta Najeriya NUT da kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi (NULGE) na Onso sun kauracewa zaben da aka yi har Ademola ya yi nasara.

A cewar ƙungiyoyin da suka zaɓi sabon shugaban NLC na Ondo, sun yi haka ne saboda tsohon shugaban ƙungiyar, Victor Amoko ya yi ritaya daga aiki.

Da yake martani Amoko wanda mamba ne a kungiyar malamai NUT ya ce yana nan daram a matsayin shugaban kungiyar NLC ta Ondo saboda har yanzu yana kan aiki.

"Ban yi ritaya ba, gwamnan Ondo ya tsawaita wa'adin wasu ma'aikata (malamai) kuma ina cikinsu, sun ce ba zasu bari na ci gaba da zama a matsayin shugaban NLC ba.
"Har yanzu ina aiki kuma hakan ya sa na zama mamban NLC, sun tura wasiƙa ga NLC ta ƙasa amma babu wata amsa har yanzu, ina nan daram a shugabancin NLC."

Gwamnatin Tinubu ta shirya ƙara albashi

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana ƙwarin guiwar cewa za a warware batun sabon mafi karancin albashi nan da makon gobe.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris da takwararsa ƙaramar ministan kwadago Nkeiruka Onyejeocha ne suka bayyana haka a Abuja.

Asali: Legit.ng

People are also reading