Home Back

"Za Mu Gama da Su": Sanata Ya Yi Wa Tinubu Alkwarin Murkushe PDP a Zaben da Za a Yi

legit.ng 2024/10/6
  • Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya yi tsokaci kan zaben jihar Edo da ake shirin gudanarwa a watan Satumba
  • Oshiomole ya fadawa Bola Tinubu tabbacin APC za ta lashe zaben gwamna da za a yi kan jam'iyyar PDP a jihar
  • Sanatan ya kuma yi fatali da jita-jitar cewa APC ce ta yi manaƙisa a kotu ta rusa zaben fidda gwanin jami'yyar PDP

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole ya sha alwashin lashe zaben gwamnan jihar Edo.

Oshiomole ya ce duk da rusa zaben fidda gwanin jami'yyar PDP da kotu ta yi a jihar, ba za su yi wasa da damar ba.

Oshiomole ya yiwa Tinubu alkawarin lashe zaben Edo
Adams Oshiomole ya bugi kirji kan zaben jihar Edo. Hoto: Adams Oshiomole. Asali: Facebook

Edo: Oshiomole ya bugi kirji kan zabe

Sanatan ta bayyana haka ne ga ƴan jaridu bayan ganawa da Bola Tinubu a fadar shugaban da ke Abuja, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya ce yana da tabbacin cewa dan takarar APC, Sanata Monday Okpebholo zai yi nasara kan Asue Ighodalo na PDP.

"Mene ya saka za mu damu da wani rakube-rakube, za mu kayar da Asue Ighodalo ko yaushe."

- Adams Oshiomole

Sanatan ya kuma yi magana kan rikicin jam'iyyar PDP da ke faruwa inda ya ce suna rasa mambobinsu zuwa APC.

Oshiomole ya ce ya zo ganin Tinubu ne domin ci gaba da sanar da shi halin da ake ciki game da kamfen APC a jihar.

Edo: Musabbabin ziyarar Oshiomole ga Tinubu

"Mun kawo masa ɗan takara da mataimakinsa domin fayyace masa halin da ake ciki a kamfen zabe."
"Muna ci gaba da karbar sabbin tuba, a makon jiya a karamar hukuma ta duka sauran ƴan jam'iyyar PDP sun koma APC."

- Adams Oshiomole

Oshiomole ya kuma karyata zargin cewa APC ce ta shirya manaƙisa aka rusa zaben fidda gwanin jami'yyar PDP.

Kotu ta rusa zaben fidda gwanin PDP

Kun ji cewa kotu ya yi hukunci kan korafin da aka yi game zaben fidda gwanin jami'yyar PDP a jihar Edo a watan Faburairun 2024.

Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben da aka gudanar a watan Faburairun 2024 da Asue Ighodalo na jam'iyyar PDP ya yi nasara.

Asali: Legit.ng

People are also reading