Home Back

Masu Zargin Uba Sani Kan Bashin el-Rufa’i Sun Jahilci Aikin Majalisa – Barista Bello

leadership.ng 2024/5/17
uba sani

An bayyana cewa dukkanin jama’a da ke zargin Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Malam Uba Sani da cewa da goyon bayansa tsohon gwamna, Malam Nasiru el-Rufa’i ya ciyo bashin da ake bin jihar sun jahilci aikin majalisa.

Mataimaki na musamman ga Gwamna Uba Sani kan harkokin masarautu, Honor-abul Barista Ibrahim Bello Rigachikum ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.

Barista Bello wanda tsohon dan majalisar tarayya ne wanda ya wakilci karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna ya kara da cewar alfarma ce Uba Sani ya nema a lokacin yana sanata a gaban majalisa domin ganin an samu bashin, saboda kyau-tata zato da yake da shi na za a aiwatar da ayyukan ciyar da Jihar Kaduna gaba, bai ga wadannan kudi ba, ba ta hannunsa suka shigo ba.

Dangane da ayyukan raya jiha da gwamna Uba Sani ke yi a Jihar Kaduna kuwa, Barista Bello ya ce a tarihin jihar ba a taba samun jajirtaccen gwamna kamar Sana-ta Uba Sani ba, duk da kalubale da ya fuskanta a farkon hawa kujerar mulki na kiki-kakar shari’ar zabe bai hana shi aiwatar da ayyukan ciyar da jama’ar Jihar Kaduna gaba ba.

People are also reading