Home Back

Abba Zai Kammala Muhimman Ayyukan da Kwankwaso Ya Fara, Ganduje Ya Yi Biris da Su

legit.ng 3 days ago
  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai cigaba da wasu ayyuka da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fara
  • Abba Kabir Yusuf ya ce Rabi'uKwankwaso ya fara ayyukan a lokacin da yake gwamna amma Abdullahi Umar Ganduje ya yi biris da su
  • Babban daraktan yada labaran gwamnatin jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya bayyana lamarin ga manema labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamantin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf za ta cigaba da wasu ayyukan da Rabi'u Kwankwaso ya fara a lokacin mulkinsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an kammala shirye-shiryen fara ayyukan amma Abdullahi Ganduje ya yi watsi da su.

Abba Kabir
Abba zai cigaba da ayyukan Kwankwaso. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da Abba zai kammala a Kano

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Rabi'u Kwankwaso ya fara ayyukan hanya a ƙananan hukumomin jihar 44.

Gwamnan ya ce an yi shirin yin hanyoyi masu nisan kilomita 5 a kowace karamar hukuma a lokacin Kwankwaso amma Ganduje ya watsar da shirin.

Gwamna Abba ya zauna da yan kwangila

Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya ce gwamna Abba ya zauna da yan kwangilar da aka ba aikin domin duba yadda za a cigaba.

Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa yan kwangilar cewa ya shirya tsaf domin ganin an kammala ayyukan a kan lokaci.

Za a kammala ayyukan Kwankwaso

Bayan tattaunawar da gwamna Abba ya yi da yan kwangilar sun amince da komawa domin cigaba da ayyukan a mako mai zuwa.

Gwamnan ya ba ma'aikatar raya ƙasa da tsare-tsaren gari umurnin gaggauta kammala shirin cigaba da ayyukan a kan lokaci.

Abba ya biya 'yan fansho a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ƙaddamar da shirin biyan kuɗaɗen giratuti kashi na biyu a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya ƙaddamar da biyan kuɗaɗen waɗanda sun kai Naira biliyan 5 daga shekarar 2016 zuwa 2019.

Asali: Legit.ng

People are also reading