Home Back

Yajin Aiki: Kungiyar MURIC ta Gano Abin da ya Faru da Jirgin Maniyyatan Aikin Hajji

legit.ng 2024/7/3
  • Kungiyar kare hakkin musulmi ta kasa (MURIC) ta gargadi kungiyar kwadago ta kasa ta gaggauta janye yajin aikin gama gari da ta fara a ranar Litinin
  • Daraktan kungiyar na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi gargadin biyo bayan yadda ya bayyana cewa yajin aikin zai kawo tsaiko babba ga jigilar alhazai
  • Shugaban ya yi takaici matuka kan yadda mambobin kungiyar suka juyar da wani jirgi da ya kamata ya dauki maniyyata aikin hajji zuwa Saudiyya ba fasinja

Abuja- Shahararraiyar kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya (MURIC) ta bayyana takaici kan yadda yajin aikin kungiyar kwadago ta NLC zai kawo cikas ga maniyyatan aikin hajjin bana.

Daraktan kungiyar ta kasa, Farfesa Ishaq Akintola ya yi takaici matuka kan yadda mambobin kungiyar kwadago suka tilastawa jirgin maniyyatan aiki hajji tashi ba maniyyaci ko daya.

NLC HQ
Kungiyar MURIC ta nemi a janye yajin aiki saboda jigilar alhazai Hoto: NLC HQ/ National Hajj Commission of Nigeria Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa farfesa Akintola ya koka kan halin da jigilar aikin hajjin bana zai fada matukar aka ci gaba da yajin aikin.

‘Lokacin yajin aiki bai kyautu ba,’ Akintola

Kungiyar kare hakkin musulmi ta bayyana lokacin da kungiyar NLC ta zaba na fara yajin aiki a kasar nan ba dace ba, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan kungiyar farfesa Ishaq Akintola ya bayyana cewa babu yadda za a yi NLC ta ce bata san cewa a wannan lokaci ne ake jigilar alhazan bana zuwa Saudiyya ba.

Ya ce yanzu haka iyalan maniyyatan aikin hajjin ban ana cikin fargabar makomarsu matukar aka ci gaba da yajin aikin, tare da hana jirage tashi da sauka.

Daraktan ya gargadi kungiyar kwadago ta gaggauta janye yajin aikin ko ta fuskanci fushin musulmi a fadin kasar nan.

Farfesa Akintola na ganin son rai ne a jefa ibadar musulmi sama da 60,000 cikin garari saboda matsalar da ake fuskanta a cikin Najeriiya.

MURIC ta fadi matsayarta kan 'yan siyasa

Mun ruwaito muku yadda kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya ta yi barazanar barranta kanta da duk wani dan siyasar da zai amfanar da musulmin kasar nan ba.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana matsayarsu, tare da Allah wadai da halin da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola ya nuna, tare da barranta musulmi da shi.

Asali: Legit.ng

People are also reading