Yajin Aiki: Kungiyar MURIC ta Gano Abin da ya Faru da Jirgin Maniyyatan Aikin Hajji
Abuja- Shahararraiyar kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya (MURIC) ta bayyana takaici kan yadda yajin aikin kungiyar kwadago ta NLC zai kawo cikas ga maniyyatan aikin hajjin bana.
Daraktan kungiyar ta kasa, Farfesa Ishaq Akintola ya yi takaici matuka kan yadda mambobin kungiyar kwadago suka tilastawa jirgin maniyyatan aiki hajji tashi ba maniyyaci ko daya.
Daily Trust ta wallafa cewa farfesa Akintola ya koka kan halin da jigilar aikin hajjin bana zai fada matukar aka ci gaba da yajin aikin.
Kungiyar kare hakkin musulmi ta bayyana lokacin da kungiyar NLC ta zaba na fara yajin aiki a kasar nan ba dace ba, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan kungiyar farfesa Ishaq Akintola ya bayyana cewa babu yadda za a yi NLC ta ce bata san cewa a wannan lokaci ne ake jigilar alhazan bana zuwa Saudiyya ba.
Ya ce yanzu haka iyalan maniyyatan aikin hajjin ban ana cikin fargabar makomarsu matukar aka ci gaba da yajin aikin, tare da hana jirage tashi da sauka.
Daraktan ya gargadi kungiyar kwadago ta gaggauta janye yajin aikin ko ta fuskanci fushin musulmi a fadin kasar nan.
Farfesa Akintola na ganin son rai ne a jefa ibadar musulmi sama da 60,000 cikin garari saboda matsalar da ake fuskanta a cikin Najeriiya.
Mun ruwaito muku yadda kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya ta yi barazanar barranta kanta da duk wani dan siyasar da zai amfanar da musulmin kasar nan ba.
Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana matsayarsu, tare da Allah wadai da halin da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola ya nuna, tare da barranta musulmi da shi.
Asali: Legit.ng