Home Back

Minista Ya Kaddamar Da Taron Horas Da ‘Yan Jarida Kan Yaƙi Da Aƙidun Ta’addanci

leadership.ng 3 days ago
Minista Ya Kaddamar Da Taron Horas Da ‘Yan Jarida Kan Yaƙi Da Aƙidun Ta’addanci

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da taron horas da ‘yan jarida na kwana biyu kan inganta rahotonni domin daƙile aƙidar ta’addanci.

An buɗe taron ne a ranar Talata a Abuja a Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA), Malam Nuhu Ribadu.

A jawabinsa, Idris ya yaba wa Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) da ONSA bisa irin ingantattun matakan da suka ɗauka na yaƙi da ta’addanci, ciki har da ayyukan ceto da dama da ba a bayyana ba.

Ya bayyana muhimmancin sadarwar da kafafen yaɗa labarai da suke yi a kai a kai, wanda hakan ke taimaka wa jama’a su fahimci al’amuran ta’addanci da tsaron ƙasa.

Ya ce: “Kafofin yaɗa labarai na da ƙarfi sosai wajen yin tasiri ga mutane da kuma inganta zaman lafiya.”

Ministan ya jaddada cewa ko dai ‘yan jarida na iya cutarwa ko kuma su taimaka wajen yaƙi da tsauraran aƙidu inda ya ƙara da cewa kyakkyawan rahoto zai iya ilimantar da jama’a domin su guje wa ta’addanci.

Ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa ba da sahihan labarai da ke cin karo da saƙwannin ‘yan ta’adda da kuma nuna nasarorin shirye-shiryen NCTC da ONSA waɗanda ke taimakawa wajen hana tayar da zaune tsaye da sake dawo da tsofaffin ‘yan ta’adda.

Ya kuma buƙaci ‘yan jarida da su yi aiki tare da masana harkokin tsaro, masana ilimin zamantakewa, masana ilimin halayyar ɗan’adam, da shugabannin al’umma don samar da ra’ayi mabambanta game da ta’addanci da hanyoyin sa.

Idris ya ce yin amfani da bayanai da bincike na iya sa labaran su su zama abin dogaro.

Ya sake jaddada goyon bayan Gwamnatin Tinubu ga aikin jarida, tare da yin alƙawarin ci gaba da bayar da sahihan bayanai na yau da kullum, da damarmarkin horaswa.

People are also reading