Bayan Rigimar Aurar da Marayu a Niger, Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Auren Mata 105 a Zamfara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Dan Majalisar Tarayya daga jihar Zamfara ya dauki nauyin aurar da mata marayu 105 a jihar.
Hon. Abdulmalik Zubairu da ke wakiltar mazabar Bungudu/Maru ya dauki matakin domin tallafawa matan wadanda ƴan bindiga suka hallaka Iyayensu.
Abdulmalik ya bayyana haka ne bayan daura auren da Sheikh Liman Musa Kura ya jagoranta a garin Bungudu, kamar yadda ya tabbatar a shafin Facebook.
Ɗan Majalisar ya ce ya yi hakan ne domin rage musu dawainiya ganin cewa iyayensu sun rasu.
Ya ce a Musulunci iyaye ne ke da alhakin daukar nauyin auren ƴaƴansu amma tun da marayu ne ya dauke musu wannan wahalar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Abdulmalik ya ce ya sayi gadaje da kujeru da sauran kayayyakin daki ga ma'auratan domin bikin cika shekara daya a Majalisa.
Daga bisani ya tallafawa ma'auratan da N100,000 da kuma N50,000 domin kula da kansu bayan sun yi aure.
Kun ji cewa Kakakin Majalisar jihar Niger ya dauki nauyin auren mata marayu wanda ya jawo cece-kuce a fadin Najeriya.
Kakakin Majalisar ya dauki nauyin auren wasu mata marayu 100 inda Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta maka shi a kotu kan haka.
Kennedy-Ohanenye ta ce hakan ya saba ka'ida inda ta bukaci koya musu sana'o'i madadin daura musu aure a wannan lokaci.
Asali: Legit.ng