Katsina: An Kama Mutum 2 da Hannu a Sace Mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sanda ta cafke mutum da ake zargin suna da hannu a sace mahaifiyar fitaccen mawanin siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne y bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Jumu'a.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ASP Abubakar ya ce yanzu haka waɗanda ake zargin suna hannun jami'ai ana ci gaba da bincike a kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ofishin ƴan sanda na Ɗanja ya samu rahoton cewa masu garkuwa sun shiga gidan Hajiya Halima Adamu da ke garin Kahutu da misalin ƙarfe 1:30 na daren yau Jumu'a, suka tafi da ita.
"Nan take jami'an ƴan sanda suka nufi wurin da lamarin ya faru da niyyar kama masu hannu a harin gami da ceto matar cikin ƙoshin lafiya.
"A binciken da suka yi ne ƴan sandan suka kama mutum biyu da ake zargi, a halin yanzu muna kan aiki za mu sake fitar da bayanai a lokacin daya dace."
- ASP Abubakar Sadiq Aliyu.
Rarara dai fitaccen mawakin siyasa kuma ya taka rawa wajen tallafa takarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu musamman a garuruwan Hausawa.
Dauda Kahutu ya riƙe muƙamin shugabam mawakan shugaban ƙasa a lokacin muƙkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A ɗazu dai kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Nasiru Mu'azu ya ce ƴan bindiga sun bi ta bayan gida ba tare da kowa ya sani ba, sun sace mahaifiyar Rarara a Kahutu
A rahoton The Nation, ya ce an tura ƙarin jami'an tsaro domin su bi sawun maharan da nufin ceto dattijuwar.
Asali: Legit.ng