Home Back

Shari’ar da ake min bita da kullin siyasa ne – Donald Trump

dailynews24.ng 2024/5/16
Donald Trump
Donald Trump

Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce shari’ar da ake masa rashin adalci ne da bita da ƙullin siyasa, bayan da ya kasance tsohon shugaban ƙasar na farko da ya fuskanci tuhuma ta wani mugun laifi a gaban kotu.

Wannan shari’a ta tarihi kasancewar Trump shugaban Amurka na farko da ke fuskantar tuhuma a kan wani babban laifi, ta fara ne da, ƙalubale na zaɓar masu taimaka wa alƙali yanke hukunci inda aka riƙa sallamar wadanda suka bayyana cewa abu ne mawuyaci su iya zama ƴan baruwan mu wato ba tare da nuna son-kai ba a shari’ar inda alƙali ya riƙa sallamar su ɗaya bayan ɗaya har ta kai ga zaɓar waɗanda za su yi aikin su kusan 32, waɗanda su ma aka riƙa yi musu tambayoyi na kwakwa ɗaya bayan ɗaya.

A yayin zaman shari’ar Mista Trump ya kasance shiru a kotun, in ban da magana da yakan yi da lauyoyinsa, jifa-jifa fuskarsa murtuke, inda duk tsawon zaman kalma uku kawai ya furta, ga alƙalin kotun Kolin ta New York, Mai Sharia Juan Merchan – a lokacin da ya tambaye shi game da yadda ake buƙatar mutum ya kasance a kotu – kalmar kuwa duka ita ce, yes- wato Eh.

To amma kuma a wajen kotun Mista Trump tun da farko ya bayyana wa manema labarai cewa shari’ar, shirme ce kawai, kuma wani hari ne a kan Amurka.

Kuma waɗannan kalamai sun ɗauki ɗan lokaci ana muhawara a kotun yayin zaman.

A shari’ar dai ofishin babban mai gabatar da ƙara na gundumar Manhattan na zargin Mista Trump da cewa ya umarci tsohon lauyansa Micheal Cohen ya biya wata mata Ms Daniels dala dubu 130.

Domin rufe bakinta a kan wata baɗala ta lalata da ake zarginsa da aikatawa wadda ya musanta an yi.

Masu gabatar da ƙara sun ce ya yi hakan ne domin zaɓen 2016.

Ana tunanin shari’ar za ta ɗauki tsawon watanni ana fafatawa inda ake buƙatar mista Trump ya ksance a cikin kotun tsawon zaman shari’ar.

Editan BBC a Arewacin Amurka ya ce shari’ar da kuma lokacin da za a ɓata ana yin ta, na iya yin babban tasiri a zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba.

People are also reading