Home Back

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Neman Fatattakar Shugaban EFCC Daga Mukaminsa

legit.ng 2024/7/3
  • Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da korafin neman sallamar shugaban EFCC, Ola Olukoyede daga mukaminsa
  • Wani lauya mai suna Victor Opatola shi ya ke kalubalantar nada Olukoyede a matsayin shugabnn hukumar
  • Opatola ya ce Olukoyede ba shi da kwarewa na tsawon shekarun da ya kamata ya kasance shugaban hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan korafin neman korar shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede.

Kotun ta yi fatali da neman sallamar Olukoyede bayan wani lauya, Victor Opatola ya kalubalnci Bola Tinubu kan nadin Olukoyede.

Alkalin kotun Mai Shari'a, Obiora Egwuatu shi ya dauki wannan mataki inda ya ce korafin ya rasa hujjoji a shari'ance, cewar Daily Nigerian.

Lauyan da ke kalubalantar nadin Olukoyede ya ce shugaban hukumar ba shi da kwarewa na shekarun da ake bukata.

Daga cikin wadanda ake karar akwai shugaban kasa da Majalisar Tarayya da Ministan Shari;a da kuma Ola Olukoyede.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, wadanda ake karar sun bukaci kotun ta yi watsi da korafin lauyan saboda rashin hujjoji ingantattu.

Lauyan shugaban EFCC, Olumide Fusika ya kalubalanci korafin inda ya kare Ola Olukoyede kan nadinsa.

Fusika ya ce Olukoyede ya cancanci nadin bayan rike mukamin sakataren hukumar da kuma zuwa matakin aiki na 17.

Bayan sauraran duka bangarorin biyu, Mai Sahri'a Egwuatu ya daga sauraran karar zuwa yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading