Home Back

Shin tsoffin shugabanni na tasiri wajen samun mulkin Najeriya?

bbc.com 2024/7/5
Tsofaffin shugabannin Najeriya

Asalin hoton, AFP

Siyasar ubangida wani abu ne da ya jima yana haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman a lokutan zabe, sai dai bayan ga batun ubangida akwai wasu kusoshi na kasa irin tsoffin shugabanni da ake ganin kan yi tasiri ko taka rawa a tafiyar da harkokin siyasar kasar.

Kusan kowanne dan siyasa a Najeriya baya rasa wani wanda yake yiwa biyayya haka zalika akwai tsoffin shugabanni da ake yiwa kallon masu tasiri ko bada gudunmawa wajen tafiyar da tsari na demokuradiyya.

Tun bayan dawowar mulkin demokuradiyya a shekaru 25 da suka gabata ake ganin yadda wasu 'yan siyasa da ke takara ko hankorar takara kan tattauna ko ziyarta da mu'amala da tsoffi ko shugabannin na siyasa.

A lokacin mulkin Olusegun Obasanjo akwai wadannan suka rinka ganin cewa tsohon shugaban mulkin soji Janar Ibrahim Babangida ya ba da gudunmawa wajen a za shi a kujerar mulki.

Sannan akwai wasu 'yan siyasa na wannan zamani irinsu Peter Obi na jam'iyyar Labour da ake gani ko zargi Obasanjo ya dan marasa masa baya a takararsa ta zaben 2023.

To sai dai wani abu da ya fi jan hankali a wannan lokaci shi ne ganin yadda mutanen da ake ganin na da karfi a siyasar Najeriya ke bibbiyar tsoffin shugabannin ana tattaunawa.

Me aka tattauna?

Duk da dai babu wani da zai iya fito a takamaimai ya ce ga abubuwan da ake tattaunawa da dalilan wasu ziyarce-ziyarce da ake gani.

Akwai Naziru el-rufai da ya gana da tsohon shugaba Muhammadu Buhari a kwanakin baya. Sannan akwai lokacin da aka ganinshi tare da Olusegun Obasanjo.

Sai gashi a wannan lokaci dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Atiku Abubakar ya ziyarce tsohon shugaba Muhammadu Buhari duk da cewa sun yi takara tare a inuwar jam'iyya daban-daban, kodayake a 2011akwai kyakyawan alaka a tsakaninsu.

Sannan Peter Obi yana ta kara-kaina da gudanar da wasu ayyukan da ke kama da neman hadin-kai ko shirya kansa gabannin zaben 2027.

Masana harkokin siyasa sun ce idan aka yi la'akri da tasirin siyasar kasar kusan duk wannan ba wani abu ne sabo ba. Hany ce ta kulla kyakyawan alaka da neman gwada sa'a kan wasu bukatu.

Ta ya ya tsofoffin shugabanni ke tasiri?

Masana harkokin siyasa irinsu Farfessa Kamilu Sani Fagge daga Jami'ar Bayero da ke jadadda cewa ire-iren wannan ziyara ko 'yar kebiya tsakanin 'yan siyasa ba bakon abu ba ne.

Farfesa ya bada misali da wasu fitattun 'yan siyasa a baya da suka nemi takara da amfani da salon neman goyon-baya daga wasu tsofoffin shugabannin kasa, wajen ganin sun yi tasiri.

Ya ce ana kokari ne na neman goyon-bayan manyan 'yan siyasa duk da cewa kowa na da nashin goyon-baya.

"Galibi akan yi hakan ne saboda idan takara ya zo ko lokacin zabe ba zai yi suka ba ko bata dan takara".

Sannan salon ne na hadin-kai ko hada karfi da karfe wajen tafiya tare, saboda 'yan siyasa da zarran an gama zabe hankoronsu shi ne zabe na gaba.

Farfesan ya ce sirrin takara ko siyasa ba sai ana jam'iyyar guda ba, saboda akwai wasu abubuwa da hikima da kowanne dan siyasa ke da ita wajen bada gundumawa da ke tasiri matuka a lokutan zabe.

Ya bada misali zaben 2023 da Peter Obi ya samu goyon-bayan Obasanjo, don haka idan wadannan mutane ne masu karfi da tabbas idan an yi amfani da su ana ganin tasiri a siyasa ko takara.

Farfesa ya ce duk da cewa cin zabe ba wai dole sai da wani tsohon shugaban kasa ba, akwai wani salo ko tasiri na jan hankalin magoya-baya su yi koyi ko aiwatar da abin da suke ganin shi ubangidansu ke yi.

Sannan ana hakan wajen neman taimako daga ketare da kungyoyi. Saboda a wurare daban-daban idan aka samu irin wannan suna yiwa mutum hanyar kudi da goyon-bayan kasashe.

Farfesan ya kuma tabo batun masu hannu da shuni da za su iya amfani da tasirinsu wajen ganin dan takara ya kai labari, muddin an tsaya masa.

Babu jam'iyya a wannan harkar

Farfesa Kamilu ya tusanar da cewa akwai shekaru na siyasa da rayuwa da idan mutum ya kai ko rikakken dan siyasa to yakan juya akalar wasu tsare-tsare.

Kamilu ya ce kawai abin takacin shi ne yadda galibi kowa bukatunsa da ribar kanshi kai suke bai wa fifiko a lokuta da dama na siyasa.

Masanin ya ce siyasa kasuwar bukata ce kowa idan zai samu riba ko biyan bukata yake karkata.

Don haka a cewarsa akwai rawar da kowanne dann siyasa ba wai tsoffin shugaban kasa kadai ba ke takawa idan aka zo batun zabe da takara.

People are also reading