Home Back

Bentancur ya nemi afuwa wajen Son kan tuntuben kalamai

bbc.com 2024/7/8
Son and Bentancur

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Tottenham, Son Heung-min ya sanar cewar takwaransa Rodrigo Bentancur ya nemi afuwarsa, bayan tuntuben kalamai da ya yi.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin a Uruguay, mai gabatar da shirin ya tambayi Bentancur ko zai bashi rigar Tottenham?

Sai ya bayar da amsa da cewa ''Sonny? za ta iya zama ta dan uwan Sonny ce, domin dukkansu kamarsu iri daya ce.''

Daga baya Bentancur ya nemi afuwa a kafarsa ta sada zumunta a Instagram, inda ya ce ''bai kamata da barkwancin da na yi ba mara kyau ne''.

Son kyaftin din Tottenham ya sanar cewar na tattauna da Lolo ''Ya yi kuskure ya kuma gane hakan, daga baya ya kuma nemi afuwa.''

''Lolo ba zai taba fadar kalaman da zai ci zarafi ba. Mu 'yan uwa ne, babu abinda zai sauya.''

''Mun wuce irin wannan lamarin, kanmu a hade yake, za mu hadu a wasannin atisayen tunkarar kakar da za mu shiga, domin kai Tottenham matakin gaba.''

People are also reading